logo

HAUSA

'Yan Sama Jannati Da Ke Haskawa A Tashar Sararin Samaniyar Kasar Sin

2022-02-08 10:19:39 cri

A makon da ya wuce, mun gabatar muku wani labari game da Wang Yaping, 'yar sama jannatin kasar Sin ta farko da ta fara tafiya a wajen kumbon, inda ta kafa wani sabon tarihi a masana'antar sararin samaniyar kasar Sin, da kuma ba da gudummawar "kwarewar mace ‘yar sama jannati" ga bunkasuwar masana'antar a duniya baki daya. Yanzu bari mu ci gaba da kawo muku labari ne game da wannan baiwar Allah.

Kafin Wang Yaping, tun daga shekarar 1984, akwai mata guda 15 a wasu sassan duniya duniya, da suka taba gudanar da ayyukan zagaye a wajen kumbo. A wannan karon, fitowar Wang Yaping daga cikin kunbom ya kuma jawo hankalin duniya da kuma yabawa.

Irin wannan nasarar da aka cimma, ta kara karfin kasar Sin a fannin bincike sararin samaniya. Game da aikin shigar da 'yan sama jannati mata cikin ayyukan zuwa sararin samaniya, tawagar ayyukan Shenzhou-13 ta yiwa kumbo da tashar sararin samaniya cikakken shiri. Kakakin hukumar kula da sararin samaniyar kasar Sin, kuma mataimakin darektan ofishin injiniyan sararin samaniyar kasar Lin Xiqiang, ya bayyana cewa, tawagar ta Shenzhou-13 ta yi nazari kan halaye na zahiri da bukatu na 'yan sama jannati mata, tare da tsara shirin musamman dake dora muhimmanci kan tabbatar da zaman rayuwa da kiwon lafiya, ta yadda za a ba da tabbaci ga 'yan sama jannati mata, don su saba da yanayin zama da aiki yadda ya kamata a cikin dogon lokaci.

'Yan Sama Jannati Da Ke Haskawa A Tashar Sararin Samaniyar Kasar Sin_fororder_090723261ucr

Dangane da samun horo, 'yan sama jannati mata da maza suna amfani da ma’auni iri daya ne. A lokacin da ake yin horo na tsawon lokaci a karkashin ruwa, 'yan sama jannatin na bukatar sanya rigar samun horo mai nauyin kilogiram 200 da za su shafe tsawon sa'o'i shida ko bakwai, kuma yana da nauyi sosai. Domin girman jikinta bai kai na 'yan sama jannati maza ba, Wang Yaping ba za ta iya sarrafa rigar ta sararin samaniya ba. Don haka, tana bukatar karfi ninka sau biyu bisa na 'yan sama jannatin maza don kammala aikin.

Domin rage gibin dake tsakaninta da 'yan sama jannati maza, sai ta rika yin horo akai-akai. Bayan kowane horo, ko da yake ta gaji sosai, amma Wang Yaping tana farin ciki sosai, saboda kwarewarta ta kara inganta, kuma tana kara kusantar tabbatar da mafarkinta.

"Kowa yana cike da kwarin gwiwa kan 'yan sama jannatin mata da ke fita daga kumbo, kuma ni ma ina da kwarin gwiwa." Kamar yadda Wang Yaping ta taba fada kafin soma gudanar da ayyukan Shenzhou-13. Bayan shiga tashar sararin samaniya da kuma fita daga kumbo yadda ya kamata, burinta ya cika.

Akwai wani aiki ne na musamman a zaman rayuwar Wang Yaping a tashar sararin samaniya, wato koyar da "Darasi a karo na Biyu a Sararin Samaniya" a tashar.

A yayin gudanar da ayyukan Shenzhou-10, Wang Yaping ta taba koyar da daliban firamare da sakandare miliyan 60 darasi daga Kumbon Tiangong-1. Yanzu, bayan shekaru takwas, a ranar 10 ga watan Disamba na shekarar 2021, Wang Yaping ta kara zama malama dake koyar da darasi a tashar sararin samaniya ta gabatar da shirye-shiryen bidiyo kai tsaye zuwa doron duniya, wanda ya sa mutane da yawa jin dadin kallo da jin mamaki.

'Yan Sama Jannati Da Ke Haskawa A Tashar Sararin Samaniyar Kasar Sin_fororder_9825bc315c6034a85edf4b9b76425e540923dd54d8d5

Wang Yaping ta bayyana cewa, wannan ya sa na ji mahimmancin koyarwa a sararin samaniya, yara da dama sun soma kauna da ma sha’awar sararin samaniya saboda haka, wasu dalibai suka nemi koyon fasahar injiniyan sararin samaniya, har wasu kuma sun zama abokan aikina a yanzu, wanda kuma ya sa ni alfahari.

Wang Yaping ta kara da cewa, “tashar sararin samaniya ta kasar Sin, wani gagarumin aiki ne na masana'antar sararin samaniya ta kasarmu a sabon zamani, ina sa ran gudanar da karin bincike a tashar ta kasar Sin, da kuma gudanar da binciken da ya shafi rayuwar dan Adam mai ban sha'awa a nan”

'Yan Sama Jannati Da Ke Haskawa A Tashar Sararin Samaniyar Kasar Sin_fororder_刘洋

A cikin 'yan shekarun nan, kasar Sin tana ta kara ba da horo ga 'yan sama jannati mata. Tun daga shekarar 2012, lokacin da kumbon Shenzhou-9 ya yi jigilar 'yar sama jannati ta farko Liu Yang zuwa sararin samaniya, zuwa yanzu da Wang Yaping ta yi nasarar ficewa daga kumbo, ‘yan sama jannati mata na kasar Sin sun fara taka muhimmiyar rawa a wannan fanni.

A yayin da ake kokarin tabbatar da burin kasar Sin na binciken sararin samaniya, akwai ma'aikatan kimiyya da fasaha mata da dama wadanda suke sauke nauyin dake wuyansu, suke isar da kyakkyawan kuzari na rashin jin tsoron matsaloli da neman cikar mafarki ga mata a duk fadin duniya.

'Yan Sama Jannati Da Ke Haskawa A Tashar Sararin Samaniyar Kasar Sin_fororder_src=http___imagepphcloud.thepaper.cn_pph_image_153_41_55&refer=http___imagepphcloud.thepaper

Huang Weifen, babbar mai tsara tsarin 'yan sama jannati, wadda aka fi sani da "kociya mace" ta 'yan sama jannati, ta soma shiga ayyukan zabe da horar da 'yan sama jannati kusan shekaru 30 da suka gabata. Ta taba gabatar da wani cikakken shirin horar da 'yan sama jannati a cikin watanni 3 kacal a wani yanayin da ake ciki na rashin tsari, kayan aiki, da fasahohin ba da horo. A karkashin jagorancinta, tsarin horar da 'yan sama jannatin kasar Sin ya bunkasa matuka.

'Yan Sama Jannati Da Ke Haskawa A Tashar Sararin Samaniyar Kasar Sin_fororder_容易

Babbar mai tsara roka mai daukar kayayyaki samfurin Long March 2F Rong Yi, tana jagorantar tawagar nazari don gudanar da bincike kan muhimman fasahohin roka na zamani na kasar ta Sin, kuma an samu babban ci gaba. Game da ayyukansu, kamar yadda ta ce, “A wannan lokacin, rayuwar ‘yan sama jannatin ta dogara akan mu.”

'Yan Sama Jannati Da Ke Haskawa A Tashar Sararin Samaniyar Kasar Sin_fororder_吴昊

Wu Hao, mai jagorantar ayyukan zirga-zirgar ‘yan sama jannati a wajen kumbon Shenzhou 13 karo na farko, ita ce kuma mace daya tilo mai koyarwa a cikin rukunin horar da ayyukan nan. Wu Hao ta kan ce, "'Yan sama jannati suna da kwarewa sosai. A matsayinmu na malaman su, mu ma dole ne mu yi aiki tukuru don ganin mun inganta sosai."

Bisa kokarin da ake na gina tashar sararin samaniya, "karfin mata" zai kara haskakawa a cikin sararin samaniyar.