logo

HAUSA

Kasar Sin ta bukaci kwamitin Sulhu na MDD ya dauki dabarun nazartar tasirin takunkumai

2022-02-08 10:18:17 CRI

Kasar Sin ta bukaci kwamitin Sulhu na MDD ya dauki dabarun nazartar tasirin takunkumai_fororder_220208-Chinese envoy-Faeza2

Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya bukaci kwamitin Sulhu na MDD ya dauki dabarun nazarin tasirin takunkumai cikin tsanaki, yana mai tabo matsalolin da takunkuman da aka kakabawa Korea ta Arewa suka haifar.

Zhang Jun ya bayyana haka ne yayin muhawarar kwamitin sulhu na majalisar mai taken “batutuwan da ke da alaka da takunkumai: kare aukuwar matsalolin jin kai da ma wadanda ba a yi tsammani ba.”

Ya ce yayin da dukkan kasashen kwamitin ke da hakkin aiwatar da takunkuman da kwamitin ya sanya da zuciya daya, matsayar kasar Sin kan wannan batu shi ne, kwamitin ya rika nazartar tasirin takunkuman.

Ya kara da cewa, cikin shekaru 20 da suka gabata, an yi ta fadada kakaba takunkumai a kwamitin. Yana mai cewa, ba za a iya watsi da munana tasirinsu kan batutuwan jin kai da rayuwar jama’a ba, tare kuma da tsaikon da suka haifar ga habakar tattalin arziki da harkokin jama’a da kasashen da aka kakabawa takunkuman. (Fa’iza Mustapha)