logo

HAUSA

Afrika ta Kudu ta amince da amfani da riga kafin cutar COVID-19 na kamfanin Sinopharm

2022-02-08 10:52:52 CRI

Afrika ta Kudu ta amince da amfani da riga kafin cutar COVID-19 na kamfanin Sinopharm_fororder_220208-South Africa approves Sinopharm-Faeza3

Hukumar tantance ingancin magunguna na kasar Afrika ta Kudu (SAHPRA), ta amince a yi amfani da riga kafin cutar COVID-19 na Sinopharm a kasar.

Hukumar ta bayyana a jiya cewa, za a iya yin amfani da riga kafin kan mutanen da shekarun haihuwa ya fara daga 18.

Yayin da ake kiran riga kafin da Sinopharm a fadin duniya, za a kira shi da MC Pharma a Afrika ta Kudu, saboda dole ne kamfanonin kasashen waje su yi amfani da kamfanonin cikin gida, idan suna neman hukumar ta SAHPRA ta amince da alluransu na riga kafi.

Hukumar ta kuma yi wa riga kafin Comirnaty na kamfanin Pfizer regista, wanda a baya aka yi masa regista domin amfanin gaggawa. An ba Comirnaty lasisin amfani kan mutane shekaru 12 zuwa sama.

A baya dai, riga kafin na Pfizer ya samu amincewar amfanin gaggawa, wanda ya ba da damar amfani da kayayyakinsa ba tare da regista ba a kasar Afrika ta Kudu. Sahalewar na baya-bayan kuma na nufin kamfanin ya samu cikakken regista. (Fa’iza Mustapha)