logo

HAUSA

An cafke mutane 19 da ake zargi da satar man fetur a Nijeriya

2022-02-08 10:47:05 CRI

An cafke mutane 19 da ake zargi da satar man fetur a Nijeriya_fororder_220208-19 arrested Nigeria-Faeza4

Hukumar tsaro ta farin kaya ta Nijeriya wato Civil Defense, ta ce ta tsare mutane 19 da ake zargi da satar man fetur a jihar Rivers dake kudancin kasar, yayin ayyukanta na baya-bayan nan na yaki da fasa bututun mai.

Shugaban hukumar a jihar Rivers, Abu Tambuwal ya ce, an kama mutane da ake zargi ne a ranekun Juma’a da Asabar tare da manyan takunan mai 3, da wani babban kwale-kwalen katako da kuma wasu kayayyakin man fetur da dama, wadanda ake zargin man diesel ne da aka hada ta haramtacciyar hanya.

Ya ce sun kama mutanen ne tare da kwace kayayyakin, a kokarnsu na taimakawa shirin gwamnatin tarayya na yaki da haramtattun matatun mai da ke zaman wani bangare dake sabbaba gurbatar muhalli a jihar.

Har ila yau, ya ce, sun kaddamar da wannan aiki ne domin kawo karshen illata halittun ruwa da amfanin gona, da malalar mai ke haifarwa biyo bayan fasa bututan mai.

Jami’in ya ce masu bincike na hukumar, na yi wa mutane 19 da ake zargi tambayoyi, yana mai tabbatar da cewa za a gurfanar da su a gaban kotun idan aka samesu da laifin da ake tuhumarsu da shi. (Fa’iza Mustapha)