logo

HAUSA

Xi ya amsa wasikar shugaban asusun Helen Foster Snow

2022-02-07 14:59:39 CRI

Xi ya amsa wasikar shugaban asusun Helen Foster Snow_fororder_helen

A ranar 27 ga watan Janairun bana, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya amsa wasikar da shugaban asusun Helen Foster Snow na kasar Amurka Adam Foster ya rubuta masa, inda ya yi nuni da cewa, al’ummun Sinawa ba za su manta da rawar da aminansu na kasa da kasa da suka hada da Mista Edgar Snow da matarsa suka taka kan juyin juya halin kasar Sin da aikin gina kasar ba, kuma yana jinjinawa gudumowar da iyalin Helen Foster Snow ke bayarwa wajen ci gaban huldar dake tsakanin Sin da Amurka.

Kwanan baya Adam Foster ya aikewa shugaba Xi wata wasika, inda ya waiwayi rawar da madam Helen Foster Snow take takawa wajen ingiza zumuncin dake tsakanin al’ummun kasashen Sin da Amurka, shi ma ya bayyana cewa, zai ci gaba da yin kokari domin ciyar da huldar gaba yadda ya kamata. (Jamila)