Ko Gasar Olympic Ta Lokacin Sanyi Ta Beijing 2022 Za Ta Yi Tasiri A Hadin Gwiwar Kasa Da Kasa?
2022-02-07 17:11:09 CRI
Yayin da aka shiga rana ta uku tun bayan kaddamar da gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta Beijing 2022, hankulan duniyar wasanni sun karkata kan wannan babbar gasa ta kasa da kasa. A wannan karo, ’yan wasan motsa jiki kimanin dubu 3 daga kasashe da yankuna 90 ne za su halarci wasannin. Yanzu dai za mu iya cewa tafiya ta fara nisa yayin da gasar ke ci gaba da gudana kamar yadda aka tsara. Duk da irin yadda wasu kasashe ke nuna adawarsu da nufin gurgunta harkokin gasar har ma wasu na barazanar kauracewa gasar, to sai dai hakarsu ba ta cimma ruwa ba. Da dama daga cikin manyan shugabanni da masu ruwa da tsaki a harkokin wasanni na kasa da kasa suna da ra’ayin cewa gasar Olympic wata muhimmiyar dama ce ta wanzuwar hadin kan al’ummun duniya. Jama’a da dama na ganin cewa gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta Beijing 2022 wata muhimmiyar dama ce ta hada kan al’ummar duniya musamman a daidai lokacin da duniya ke tsananin bukatar hada kai don tinkarar manyan kalubaloli dake yiwa duniya barazana kamar annobar COVID-19 wacce ke ci gaba da firgita duniya daga dukkan fannoni, da batun neman farfadowar tattalin arziki, da tinkarar matsalolin sauyin yanayi da dai makamantansu. Hakika, abin da duniya ke bukata a halin yanzu shi ne hadin kai da nuna goyon baya ga juna, maimakon raba kan al’ummun duniya da kawo baraka. Wannan batu dai ya yi daidai da ra’ayin Thomas Bach, shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympic na kasa da kasa wanda ya bayyana cewa, “ya kamata mu hada kai domin kara saurin tafiya, mu kara bunkasa, mu kara karfi.” Wannan dai shi ne karo na farko da aka kaddamar da gasar Olympics ta lokacin hunturu bayan da aka kara kalmar “kasancewa tare” cikin taken Olympics. Ko shakka babu, gasar Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing, za ta ci gaba da karfafa taken Olympics, da zurfafa hadin gwiwar kasa da kasa bisa ka’idar sada zumunci da shimfida zaman lafiya. Don haka, akwai bukatar karfafa ra’ayin “kasancewa tare”, kamar yadda taken Olympics ya bayyana. (Ahmad Fagam)