logo

HAUSA

Sin ta doke Koriya ta kudu a wasan karshe na cin kofin AFC na matan Asiya

2022-02-07 14:42:36 CRI

Sin ta doke Koriya ta kudu a wasan karshe na cin kofin AFC na matan Asiya_fororder_0207-Ahmad4-AFC

Kasar Sin ta yi nasarar dagawa zuwa mataki na gaba daga 0 zuwa 2, bayan da ta doke Koriya ta kudu da ci 3 da 2 a wasan karshe na cin kofin AFC na matan Asiya, wanda aka gudanar a filin wasan D.Y. Patil dake Navi a birnin Mumbai na kasar Indiya a ranar Lahadi, inda kungiyar wasa ta kasar Sin ta lashe kofin a gasar a karo na tara.

Tun da farko a ranar Lahadin, Vietnam ta doke kungiyar wasan Taipei ta kasar Sin da ci 2-1 a wasan da suka fafata na neman share fagen shiga gasar cin kofin mata ta duniya a shekarar 2023.  (Ahmad)