logo

HAUSA

Uwargidan shugaban kasar Sin ta karfafa musayar al’adu tsakanin Sin da Ecudor

2022-02-06 17:24:36 CMG

Uwargidan shugaban kasar Sin ta karfafa musayar al’adu tsakanin Sin da Ecudor_fororder_0206-Peng-Faeza

Peng Liyuan, Uwargidan shugaban kasar Sin Xi Jinping, ta gana da takwararta ta kasar Ecuador, Maria de Lurdes Alcivar, jiya Asabar a babban dakin taron al’umma na Beijing. Tattaunawar tasu ta mayar da hankali ne kan yaki da annobar COVID-19 da musayar al’adu tsakanin kasashen biyu.

A wani daki da aka kawata da furannin Peony irin na Sin da furannin Rose irin na Ecuador, Peng Liyuan ta yi maraba da Maria Alvicar, wadda ta rako maigidanta, shugaban kasar Ecuador Guillermo Lasso, zuwa bikin bude wasannin Olympics na hunturu na 2022 a ranar Juma’a.

Da take yabawa kokarin Beijing na karbar bakuncin wasannin na Olympics duk da tasirin annobar COVID-19, Maria Alvicar ta bayyana godiyarta ga taimakon da Sin ke ba Ecuador wajen yaki da annobar tare da yi wa ‘yan wasan kasashen biyu fatan samun nasara. (Fa’iza Mustapha)

Faeza