logo

HAUSA

Kafofin yada labarun Masar sun jinjinawa bikin bude gasar Beijing Olympic

2022-02-06 17:30:21 CMG

Kafofin yada labarun Masar sun jinjinawa bikin bude gasar Beijing Olympic_fororder_0206-Masar-Olympics-Ahmad

Kafofin yada labaran kasar Masar sun yabawa bikin bude gasar wasannin motsa jiki na lokacin hunturu na Beijing, inda suka bayyana shi da cewa mai ban mamaki ne, kuma mai kayatarwa, wanda ya bayyana girman tasirin wayewar kan Sinawa da kuma rawar da wasannin ke takawa wajen tattaro al’umma wuri guda.

Jaridar Al-Ahram mallakin gwamnatin kasar Masar, ta wallafa a babban kanun labarin shafinta na intanet cewa, bikin bude gasar yana “cike da hikimomi,” kamar yadda ta jiyo daga Thomas Bach, shugaban kwamitin shirya gasar Olympic ta kasa da kasa. Yace, “a yau, zamu iya cewa, kasar Sin kasa ce ta wasannin motsa jiki na lokacin hunturu."

Kimanin mahalarta 3,000 ne suka halarci bikin bude gasar a ranar Juma’a, wanda ya samu halartar shugabannin kasashe sama da 30, da iyalan masarautu, da shugabannin kungiyoyin kasa da kasa.

An samu ruhin hadin kai a yayin bikin bude gasar, kamar yadda shafin yanar gizo na jaridar ta kasar Masar ta rawaito babban daraktan hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, yana cewa, ana fatan ruhin zai cigaba da kasancewa a hadin gwiwar kasa da kasa wajen yaki da annobar COVID-19.(Ahmad)(Kamfanin Xinhua ya samar da hoto)

Ahmad