logo

HAUSA

An bude taron koli na AU karo na 35

2022-02-05 21:15:04 CRI

Yau Asabar, an bude taron koli na shugabannin AU karo na 35 a Addis Ababa babban birnin Habasha, hedkwatar kungiyar tarayyar AU, taron na tsawon kwanaki 2. Taken taro a wannan karon shi ne “Kafa hanyar farfado da nahiyar Afrika: Ingiza bunkasuwar kwadago da al’umma da tattalin arziki.”

A bikin bude taron, shugaban kasar Senegal Macky Sall ya zama sabon shugaban karba-karba na AU.

Shugaban kwamitin kunigyar AU Moussa Faki Mahamat ya bayyana cewa, ana nuna damuwa game da halin tsaro da Afrika ke ciki. Faki ya nanata cewa, ya kamata Afrika ta nace ga manufar kasancewar bangarori daban-daban, da nacewa kan tabbatar da hadin kai tsakanin kasa da kasa mai amfani. (Amina Xu)