logo

HAUSA

Ministan Najeriya ya yaba ayyukan layin jirgin kasa da Sin ke gudanarwa

2022-02-05 17:01:31 CMG

Ministan Najeriya ya yaba ayyukan layin jirgin kasa da Sin ke gudanarwa_fororder_0205-Nigeria-Sin-Ahmad

Ministan sufurin Najeriya Rotimi Amaechi, ya yaba da ingancin ayyukan da kamfanin kasar Sin ke gudanarwa na layin dogo tsakanin Kano zuwa Kaduna, inda ya bayyana cewa, ayyukan za su samar da wata muhimmiyar dama na cigaba.

Da yake bayani game da muhimmancin amfani da kayayyakin aiki da ake samarwa a cikin gidan kasar da kuma ma’aikatan da kamfanin gine-ginen na kasar Sin ke amfani dasu, ministan yace, gwamnatin Najeriya ba kawai tana karfafa gwiwar amfani da kayayyakin aiki na cikin gidan kasar ba ne har ma tana son kamfanin ya dauki ma’aikata ‘yan asalin kasar aiki.

A cewar ministan, an tsara aikin ne ta yadda za a dinga gudanar da ayyukan jigilar fasinjoji da na kayayyaki, musamman manyan kayayyaki.

Amaechi ya ce, jahar Kano, wani muhimmin birni ne a arewacin Najeriya, kuma muhimmiyar cibiyar kasuwanci, kana aikin layin jirgin kasan zai karfafa hada hadar kasuwanci tsakanin biranen Kano da Legas cibiyar kasuwancin Najeriya.

Ministan ya bayyana fatan cewa layin dogon zai fara aiki kafin watan Mayun shekarar 2023.(Ahmad)

Ahmad