logo

HAUSA

Rawayan kogin na kasar Sin ya samu babban ci gaba a fannin kiyaye muhalli

2022-02-05 17:07:06 CMG

Rawayan kogin na kasar Sin ya samu babban ci gaba a fannin kiyaye muhalli_fororder_0205-Yellow  River-Ibrahim

Wani sabon rahoton da hukumar kula da rawayan kogi na kasar Sin ta fitar ya nuna cewa, rawayan kogi na kasar Sin, ya samu babban ci gaba a fannin kiyaye muhallin halittu, bayan da aka ci gaba da kokarin kiyaye muhalli.

Rahoton ya kuma bayyana cewa, idan aka kwatanta da sakamakon binciken zaizayar kasa ta farko da majalisar gudanarwar kasar ta gudanar a shekarar 1990, yawan zaizayar kasa a kewayen kogin ya ragu da murabba'in kilomita 202,300, wato kashi 43.51 cikin 100 a shekarar 2020, sannan yawan zaizayar kasa ya ragu da kashi 81.70 bisa dari.

Alkaluma sun nuna cewa, a shekarar 2020, fadin zaizayar kasa da aka samu a rawayan kogi, ya kai murabba'in kilomita murabba'i 262,700, wanda ya hada da zaizayar ruwa mai fadin murabba'in kilomita 191,400, da kuma zaizayar kasa mai fadin murabba'in kilomita 71,300 da iska ta haddasa.

A halin da ake ciki, adadin yadda ake kiyaye kasa da ruwa a cikin rawayan Kogi, ya karu daga kashi 41.49 a cikin 1990 zuwa kashi 66.94 a cikin shekarar 2020.

Rahoton shi ne irinsa na biyu, tun bayan da hukumar da ke karkashin ma’aikatar albarkatun ruwa ta kasar Sin ta fitar a shekarar 2010. Manufar wallafa wannan rahoto, ita ce tsara matakan kariya da amfani da albarkatun ruwa da kasa a tafkunan koguna da kara wayar da kan jama'a game da muhimmancin kiyaye ruwa da kasa a cikin al'umma baki daya.(Ibrahim)

Ibrahim