logo

HAUSA

Nazari: Omicron ba ya kaiwa ga kwantarwa a asibiti fiye da Delta

2022-02-05 17:08:25 CMG

Nazari: Omicron ba ya kaiwa ga kwantarwa a asibiti fiye da Delta_fororder_0205-Omicron-Ibrahim

Wani sabon bincike da hukumomin kiwon lafiya na kasar Portugal suka gudanar ya nuna cewa, hadarin kwanciya a asibiti, ya ragu da kashi 75 cikin 100 ga mutanen da suka kamu da nau’in Omicron na COVID-19 fiye da na Delta.

Binciken da babban darektan kula da Lafiya na kasar Portugal (DGS) da cibiyar kiwon Lafiya ta Doutor Ricardo Jorge (INSA) suka gudanar ya nuna cewa, mutanen da suka kamu da nau’in  Omicron suna da, matsakaici, da karancin yiwuwar kwanciya a asibiti, da ma karancin hadarin mutuwa sanadiyar cutar.

A cewar binciken, wannan raguwar hadarin gaskiya ne, ba kuma tare da la'akari da yawan shekaru,ko jinsi, da matsayin rigakafin maras lafiya ba. Haka kuma ko mutumin ya taba kamuwa da COVID-19 ko a'a.

An gudanar da binciken ne a kan mutanen da ke zaune a Portugal a cikin Disamban shekarar 2021.

Wadanda suka wallafa binciken, sun kuma yi gargadin cewa, nau’in Omicron yana da yiwuwar bijirewa allurar rigakafi, abin da ya sa nau’in cutar kara yaduwa, da ma kara samun wadanda suka harbu da cutar.(Ibrahim)

Ibrahim