Dangantakar Sin Da Rasha Na Kara Inganta Bayan Haduwa A Gasar Olympic Ta Lokacin Sanyi Ta 2022
2022-02-05 16:49:11 CRI
Daga CRI HAUSA
Jiya da dare ne, aka bude gasar Olympic ta lokacin sanyi karo na 24 a nan birnin Beijing. Cikin shugabannin da suka halarci wannan biki har da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin.
A wannan rana da yamma, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa mista Putin, inda ya ce, “Zuwanka wannan karo, tamkar cika alkwarin da muke yi na saduwa a bikin. Na yi imani cewa, saduwar da muke yi a yau, za ta ingiza dangantakarmu.”
A yayin ganawar tasu, hadin kai bisa manyan tsare, ya zama muhimmiyar kalma, wadda ta dace da bukatun duniya ta neman zaman lafiya da samun bunkasuwa mai dorewa, bisa la’akari da sauye-sauyen da ake fuskanta a halin yanzu.
Bangarorin biyu sun kuma fitar da hadaddiyar sanawa, don bayyana matsayinsu a fannin ra’ayin demokuradiyya da samun bunkasuwa da tsaro da zaman oda da doka da sauransu. Sanarwar ta kuma bayyana aniyyarsu ta kiyaye adalci da daidaito da ciyar da tsarin demokuradiyya gaba a dangantakar kasa da kasa. (Amina Xu)