logo

HAUSA

Gasar Olympics Ta Beijing Za Ta Karfafa Hadin Gwiwar Kasa Da Kasa

2022-02-04 15:58:36 CRI

Gasar Olympics Ta Beijing Za Ta Karfafa Hadin Gwiwar Kasa Da Kasa_fororder_220204-Sharhi-Maryam-hoto

“Ya kamata mu hada kai domin kara saurin tafiya, kasa bunkasa, mu kara karfi.” Wannan shi ne kiran da shugaban kwamitin shirya gasar wasannin motsa jiki ta Olympics na kasa da kasa Thomas Bach ya yi wa dukkanin ‘yan wasan motsa jiki. Tabbas, Gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta binin Beijing da za a bude a daren ranar 4 ga wata, za ta karfafa hadin gwiwar kasashen duniya.

Wannan shi ne karo na farko da aka kaddamar da gasar Olympics ta lokacin hunturu bayan aka kara Kalmar “kasancewa tare” cikin taken Olympics. A wannan karo, ’yan wasan motsa jiki kimanin dubu 3 daga kasashe da yankuna guda 90 za su halarci wasannin, kuma, wasannin da za su yi, da kuma lambobin yabo ta zinari da za a bayar, sun kasance mafi yawa a tarihin gasar Olympics ta lokacin hunturu. Ko shakka babu, gasar Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing, za ta ci gaba da karfafa taken Olympics, da zurfafa hadin gwiwar kasa da kasa bisa ka’idar sada zumunci da shimfida zaman lafiya.

Kana, gasar Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing tana zuwa ne,a daidai lokacin da duniya ke fuskantar matsaloli, wadanda suka hada da yaduwar annobar cutar COVID-19, da masu neman siyasantar da gasar Olympics. Sabo da haka, muna bukatar karfafa ra’ayin “kasancewa tare”, kamar yadda taken Olympics ya bayyana. Yana da kyau kasashen duniya su shiga babban jirgin ruwa, a maimakon kasancewa cikin kananan jiragen ruwa guda 190, ta yadda za a fuskanci kalubaloli cikin hadin gwiwa, da gina makoma mai haske. Kuma, wannan ita ce manufar kasar Sin ta gabatar da taken gasar wato “hadin kai tare domin amfanin gaba” a matsayin babban taken gasar Olympics ta lokacin hunturu, wanda ya dace da taken Olympics da kuma burinmu na karfafa hadin gwiwar dukkanin bil Adama. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)