logo

HAUSA

Gasar Olympic Ta Lokacin Sanyi A Beijing Ta Baiwa ‘Yan Wasan Kasashen Afrika Dama Mai Kyau

2022-02-03 16:03:11 CRI

Gasar Olympic Ta Lokacin Sanyi A Beijing Ta Baiwa ‘Yan Wasan Kasashen Afrika Dama Mai Kyau_fororder_src=http___pic.0513.org_forum_201802_16_085736md2rr9jfhhejf2ad&refer=http___pic.0513

 

 

Daga Amina Xu

Ba safai a kan yi dusar kankara a kasashe masu yanayin zafi ba, hakan ya sa da wuya ne su gudanar da wasannin kankara, amma ‘yan wasan wadannan kasashe na y in iyakacin kokarinsu don shiga gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi, duk da cewa  wani lokaci, dan wasa kadai ke wakiltar kasarsa. A duk wata gasar Olympic ta lokacin sanyi, ‘yan wasan nahiyar Afrika na karya bajimtarsu, ko da yake yanzu cutar COVID-19 ke ci gaba da yaduwa a duniya, amma hakan bai hana su zuwa gasar ba, ana yi musu lakabin Jarumi mai kadanci daga Afrika.

Tun daga shekarar 1960, Afrika ta kudu ta zama kasar Afrika ta farko da ta shiga irin wannan gasa, zuwa wannan karo ‘yan wasa 6 daga kasashen Kenya da Najeriya da Madagascar da Morocco da Eritrea. ‘Yan wasan nahiyar ba su daina kokarinsu na cimma burinsu a gasar.

Gasar Olympic Ta Lokacin Sanyi A Beijing Ta Baiwa ‘Yan Wasan Kasashen Afrika Dama Mai Kyau_fororder_src=http___www.jasmemorial.org_uploadfile_image_20180223_20180223083746_52105&refer=http___www.jasmemorial

Wannnan ne karo na biyu da Najeriya ta shiga gasar Olympics ta lokacin sanyi, a matsayin dan wasa namiji na farko a bangaren gudun dusar kankara dake wakiltar kasar Najeriya a wannan karo, Samuel Ikpefan zai yi takara a wasan cross-country. A ganinsa, wannan gasa na da ma’ana matuka, saboda za ta shaida wa duniya cewa, ko kasashen da ba sa yawan yin wasannin kankara ba za su iya shiga wannan gasa. Ya ce: “Ina farin ciki matuka don ganin mata 3 ‘yan Najeriya masu wasan sleds sun shiga gasar da aka yi a Pyeongchang, kuma shi ne abin da ya kara mana kwarin gwiwa don shiga gasar a wannan karo, kuma ya baiwa jama’ar kasar kwarin gwiwa. A ganina, akwai muhimmanci matuka don yayata wasannin kankara a yankin zafi.”

Gasar Olympic Ta Lokacin Sanyi A Beijing Ta Baiwa ‘Yan Wasan Kasashen Afrika Dama Mai Kyau_fororder_src=http___www.jasmemorial.org_uploadfile_image_20180223_20180223083711_65291&refer=http___www.jasmemorial

Ni na zanta da mamban IOC kana shugaban NOC Habu Ahmad Gumel a gabanin budewar gasar Olympics ta wannan karo, wanda ya gaya min cewa, a ganinsa komai ya yi daidai a Beijing, ana shirin tsaf don kaddamar da gasar. Gasar da za a yi a wannan karo na da babbar ma’ana ga Najeriya, saboda Najeriya ta tura ‘yan wasanta zuwa gasar sau 2 a jere, abin da ya bayyana niyyar kasar ta bunkasa wannan bangare. Haka ne, duk da cewa COVID-19 na ci gaba da yaduwa a duniya, kuma Najeriya na fuskantar kalubaloli iri daban-daban a cikin kasar, yadda NOC ya tura dan wasan da ya shiga gasar, ba ma kawai ta amince da gasar da za a yi a Beijing ba, har ma ya nuna goyon baya ga ruhin Olympic.

Ganin yadda kasashen Afrika ke kokarin cimma burinsu a cikin gasar, fuskar wasu ‘yan siyasa na kara rubewa, saboda haka suke yunkurin bata sunan gasar Olmpic ta lokacin sanyi dake tafe a Beijing da burin siyasantar da batun gasar wasanni, ba ma kawai sun yi adawa da gasar da Beijing za ta yi ba, har ma sun yi adawa da burin 'yan wasa da na jama’ar Afrika na cimma mafarkinsu a wasannin kankara har ma kokarinsu na bin ruhin Olympic.

Malam Habu Ahmad Gumel ya bayyana min cewa, yana fatan Allah ya sa a fara wannan wasa lafiya, a gama shi lafiya. Ko shakka babu, wannan shi ne burin ‘yawancin mutane, wasu ‘yan siyasa kamata ya yi su zabi hanyar da ‘yawancin mutane ke bi a maimakon yunkurin bata ta. Dusar kankara a gasar wasan Olympic da za a yi a Beijing farin fat ne, mutane ke kokarin neman cimma burinsu a cikin gasar ke iya taka a kansa. (Amina Xu)