logo

HAUSA

Xi: Sin ta shirya kaddamar da gasar Beijing 2022 gobe

2022-02-03 16:21:58 CMG

Xi: Sin ta shirya kaddamar da gasar Beijing 2022 gobe_fororder_0203-Xi-Ibrahim

Yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo yayin bude taro karo na 139 na kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa (IOC). Xi ya jaddada cewa, kasar Sin tana taka rawar gani sosai a fagen gasar wasannin Olympics, kuma tana sa kaimi ga karfafa ruhin gasar wasannin Olympics.

Xi ya ce, gobe da yamma ne, za a bude gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi na birnin Beijing na shekarar 2022, kuma hankalin duniya baki daya ya karkata kan kasar Sin. Ya kara da cewa, kasar Sin ta shirya tsaf don gabatar da wasannin Olympics mai sauki, tsaro da ban sha'awa ga duniya. (Ibrahim)

Ibrahim