Maraba Da Zuwan Gasar Olympic Mai Cike Da Tarihi
2022-02-03 16:10:17 CRI
Kawo yau Alhamis, ranar jajiberin bude gasar Olympic ta lokacin hunturu da birnin Beijing zai karbi bakunci, masu ruwa da tsaki daga sassan duniya na ci gaba da tofa albarkashin bakin su, game da fatan alheri, da kwarin gwiwa da suke da shi na gudanar da wannan gasa cikin nasara.
A baya bayan nan, shugaban kwamitin shirya gasar Olympics na kasa da kasa IOC Thomas Bach, ya shiga layin masu jaddada karfin gwiwar su ga nasarar wannan gasa. A kalaman sa, Mr. Bach ya ce “Da hadin gwiwar kowa da kowa, za mu rubuta tarihi a harkar wasanni. Beijing zai kasance birni na farko a duniya da zai karbi bakuncin gasar Olympic ta lokacin zafi da kuma ta lokacin hunturu. Kaza lika wannan gasa ta Olympic ta Beijing ta shekarar 2022, za ta kasance mabudi a sabon zamanin da muke ciki musamman a fannin wasannin lokacin hunturu.
Ko shakka ba bu, wannan gasa ta ingiza sha’awar wasannin hunturu tsakanin al’ummar Sinawa, inda a yanzu haka sama da Sinawa miliyan 300 suka shiga wasannin kankara da na dusar kankara. A yau, Sin ta zama kasar wasannin hunturu. Kuma wannan yanayi zai canza akalar wasannin kankara, tare da fadada shi tsakanin karin miliyoyin al’ummun duniya.
Gasar Olympic ta bana, na kara haskaka yadda al’ummar duniya ya kamata su yi hadin gwiwa, domin shirya wasanni na kasa da kasa, a duk wani yanayi da duniya ta tsinci kan ta ciki. Sin ta yi hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki a dukkanin sassa, domin tabbatar da nasarar wannan gasa.
Cikin kwanaki masu zuwa, ‘yan wasa daga sassan duniya da dama, za su hadu da juna, su fafata domin lashe lambobin yabo na gasar Olympic, inda za su yi tarayya cikin lumana, a kunyen Olympic da aka tanada. A hannu guda kuma, biliyoyin al’ummun duniya za su nishadantu da wannan kasaitacciyar gasa.
Fatan dukkanin mashirya gasar, da masu ruwa da tsaki, shi ne a gudanar da wasanni cikin lumana, tare da martaba juna. A hannu guda, birnin Beijing na kara maraba da duniya, zuwa kallon gasa mai kayatarwa, wadda za ta jima duniya na tunawa da ita. (Saminu Alhassan)