logo

HAUSA

Dukkanin tawagogi 91 sun kammala rajista gabanin bude gasar Olympic ta birnin Beijing

2022-02-02 17:18:11 CMG

Dukkanin tawagogi 91 sun kammala rajista gabanin bude gasar Olympic ta birnin Beijing_fororder_0202-Olympics-teams-Saminu(1)~1

Kwamitin shirya gasar Olympic ta birnin Beijing ko BOCOG a takaice, ya ce dukkanin tawagogi 91 da za su fafata a wannan gasa, sun kammala yin rajista gabanin bude gasar a ranar Juma’a mai zuwa.

Kwamitin wanda ya bayyana hakan a Larabar nan, ya kuma ce tuni ‘yan wasa da masu ruwa da tsaki, suka shirya tsaf domin tinkarar wannan gasa, inda tsakanin karfe 6 na yammacin ranar Litinin 31 ga watan Janairun da ya gabata, zuwa 6 na yammacin Talata 1 ga watan Fabarairun nan, adadin tawagogin da suka iso kasar Sin ya kai 1,750.

Alkaluman da kwamitin BOCOG ya fitar sun nuna cewa, tsakanin ranar 4 ga watan Janairu zuwa 1 ga watan Fabarairun nan, yawan mahalarta gasar da suka iso birnin Beijing ya kai mutum 12,349, kuma wasu 117 sun fita daga birnin.

Gasar Olympic ta lokacin hunturu da birnin Beijing zai karbi bakunci, na kara samun karbuwa tsakanin kafofin watsa shirye shirye na kasa da kasa, inda tsakanin ranar 4 ga Janairu zuwa 1 ga Fabarairun nan, aka budewa ‘yan jaridu, da masu daukar hotuna, da masu watsa shirye shirye 8,210 katunan aiki, wadanda za su yi amfani da su yayin wannan babbar gasa.    (Saminu)

Saminu