logo

HAUSA

Tabbas za a gudanar da gasar Olympics ta Beijing cikin yanayin tsaro

2022-02-02 19:45:32 CRI

Tabbas za a gudanar da gasar Olympics ta Beijing cikin yanayin tsaro_fororder_220202-sharhi-Maryam-hoto

“Tabbas za a gudanar da gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta Beijing cikin yanayin tsaro”, in ji Brian McCloskey, kwararren tawagar kiwon lafiya ta gasar Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing. Ya ce, birnin Beijing yana da tsarin dakile yaduwar kwayoyin cuta mai inganci, mun amince da haka.

Bayan binciken da Brian McCloskey ya yi kan tsarin dakile yaduwar kwayoyin cuta na birnin Beijing, ya nuna amincewarsa kan tsarin. A halin yanzu, ana ci gaba da fama da matsalar yaduwar annobar cutar COVID-19 a kasashen duniya, bisa bukatun kwamitin gasar Olympics na kasa da kasa, da kwamitin gasar Olympics na nakasassu, da na kwamitin gasar Olympics ta lokacin hunturu ta birnin Beijing, kasar Sin ta dauki matakai yadda ya kamata domin dakile yaduwar annoba, da tabbatar da tsaro da lafiyar jama’a.

‘Yar wasan gudun kankara cikin sauri ta kasar Amurka Maame Biney ta bayyana cewa, “a ganina, muna da tsaro a birnin Beijing, sabo da na san cewa, akwai ma’aikata da yawa dake kula da lafiya da tsaronmu.”

Shugaban sashen kula da gasar Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing na kwamitin gasar Olympics na kasa da kasa, Juan Antonio Samaranch Jr, ya bayyana cewa, ana daukar matakai masu inganci wajen hana yaduwar annoba a birnin Beijing, za a iya kiran unguwannin gasar “wuri mafi tsaro a duniya”. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)