logo

HAUSA

‘Yan bindiga sun hallaka mutane 1,192 a jihar Kaduna dake arewa maso yammacin Najeriya a 2021

2022-02-02 17:19:18 CMG

‘Yan bindiga sun hallaka mutane 1,192 a jihar Kaduna dake arewa maso yammacin Najeriya a 2021_fororder_0202-Nigeria-Saminu~1

Alkaluman hukuma sun nuna cewa, a shekarar 2021 da ta gabata, adadin mutane da ‘yan bindiga suka hallaka a jihar Kaduna dake arewa maso yammacin Najeriya, sun kai mutum 1,192, baya ga wasu karin mutum 3,348 da aka yi garkuwa da su, a hare haren barayin daji dake addabar sassan jihar ta Kaduna.

Wani rahoto game da harkokin tsaro na 2021, wanda mahukuntan jihar suka fitar, ya nuna cewa, wasu mutane 891 sun ji raunuka, kana a cikin shekarar ta bara, an yiwa mutane 45 da aka sace fyade, ciki harda masu karancin shekaru su 29.

A cewar kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro a jihar ta Kaduwa Samuel Aruwan, rahoton ya kunshi dukkanin hare hare da ‘yan bindiga suka kai a sassan jihar, ciki har da na barayin daji, da hare haren ramuwar gayya, da na masu garkuwa da mutane, da barayin shanu.

Aruwan ya kara da cewa, an yi nasarar cafke masu safarar makamai da dama, an kuma kwace tarin bindigogi da albarusai a shekarar ta bara.    (Saminu)

Saminu