logo

HAUSA

An fara mika wutar gasar Olympics a birnin Beijing

2022-02-02 17:13:03 CMG

An fara mika wutar gasar Olympics a birnin Beijing_fororder_0202-Olympic torch relay-Ibrahim~1

Yau ne, aka fara mika wutar gasar Olympics ta lokacin sanyi ta 2022, yayin da ya rage kwanaki biyu a kaddamar da gasar a hukumance.

Mataimakin firaministan kasar Sin Han Zheng, kuma mamban zaunannen kwamitin kula da harkokin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS, ya kunna wutar gasar daga wani kasko, yayin bikin kaddamar da gasar a wurin shakatawa na Olympics, sannan ya mikawa Luo Zhihuan mai shekaru 80 da haihuwa,dake zama zakaran wasannin hunturu na farko na kasar Sin.

Shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na kasa da kasa Thomas Bach, ya fada a wani sakon bidiyo cewa, a cikin 'yan kwanaki kadan ne, 'yan wasan motsa jiki na lokacin sanyi daga sassan duniya za su hallara a nan birnin Beijing, inda za su yi fafata da juna don lashe lambobin yabo. A sa'i daya kuma, za su zauna tare cikin lumana a karkashin laima guda a kauyen gasar Olympics.

An takaita bikin mika wutar gasar kuma ya gudana karkakashin tsauraran matakan kariya saboda damuwa game da cutar COVID-19.

Kimanin mahalarta 1200 ne za su halarci mika wutar, wanda zai dauki tsawon kwanaki uku ana gudanar da shi a yankuna uku na gasar, kuma za a kai ga haska kaskon a yayin bude gasar a daren ranar Juma'a.(Ibrahim)

Ibrahim