Sin za ta gudanar da gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing tare da kiyaye muhalli
2022-02-01 16:37:05 CRI
Kwanan baya, shafin yanar gizo na jaridar Münchner Merkur, ya wallafa wani bayani dake nuna kokarin da kasar Sin ke yi, na gudanar da gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi da birnin Beijing zai karbi bakunci tare da rage fitar da hayaki mai dumama yanayi, da kuma yin tsimin makamashi.
Bayan Sin ta samu izinin karbar bakuncin gasar a shekarar 2015, kasar ta kuma yi kokarin gudanar da wannan aiki na a zo a gani, har ta kai ga tsai da manufofi 119, wadanda ake amfani da su a aikin sarrafa makamashi, da gina dakuna, da gina hanyoyin zirga-zirga da sauransu.
An mai da samar da makamashi wani misali, inda dukkanin wutar lantarkin da dakunan wasanni 26 na gasar za su yi amfani da ita, ana samar da ita ne ba tare da gurbata muhalli ba. Ban da wannan kuma, dakunan da ake amfani da su a gasar, dukkansu suna samar da damar kariya ga muhalli.
Bugu da kari, shugaban hukumar IOC Thomas Bach ya bayyana cewa, kwamitin gasar na Beijing, ya dauki matakai iri daban-daban, don rage fitar da hayaki masu dumama muhalli, da kiyaye muhallin hallitu, matakin da ya zama cika alkawari da Sin ta dauka ne, game da ba da gudunmawa wajen samun bunkasuwa mai dorewa. (Amina Xu)