logo

HAUSA

'Yar Sama Jannati Da Ke Haskawa A Tashar Sararin Samaniyar Kasar Sin

2022-02-01 21:39:49 cri

Yanzu haka kumbon Shenzhou-13, wanda aka harba a ranar 16 ga watan Oktoba na shekarar 2021, ya shafe watanni uku da wani abu yana aiki a sararin samaniya. Baya ga tsawon lokacin da Shenzhou-10 da aka harba a ranar 11 ga watan Yuni na shekarar 2013 kuma ya dawo a ranar 26 ga watan Yuni na wannan shekarar. Wang Yaping, shafe fiye da kwanaki 100 tana aiki a sararin samaniya, abin da ya sa ta zama 'yar sama jannati ta farko a kasar Sin da ta shafe kwanaki sama da 100 tana kewayawa a sararin samaniya.

'Yar Sama Jannati Da Ke Haskawa A Tashar Sararin Samaniyar Kasar Sin_fororder_Wang Yaping Yar sama jannati ta Sin

Ya zuwa yanzu, 'yan sama jannatin Shenzhou-13 sun shafe fiye da watanni 3 a tashar sararin samaniyar kasar Sin, wato ke nan rabin lokacin da aka shafe a rayuwa na watanni shida a sararin samaniya.

A cikin wannan lokaci, 'yan sama jannatin kasar Sin guda uku, sun kammala wasu ayyuka masu muhimmanci, ciki har da zagaye a wajen kumbon. Wang Yaping, wadda ta je sararin samaniya a karo na biyu, ta zama 'yar sama jannatin kasar Sin ta farko da ta fara tafiya a wajen kumbon, inda ta kafa wani sabon tarihi a masana'antar sararin samaniyar kasar Sin, da kuma ba da gudummawar "kwarewar mace ‘yar sama jannati" ga bunkasuwar masana'antar a duniya baki daya.

Mafarkin Wang Yaping na zuwa sararin samaniya, ya samo asali ne daga aikin da ya shafi kumbon jigilar 'yan sama jannati na farko na kasar Sin a shekarar 2003. Bayan cimma nasarar harba kumbon Shenzhou-5, Wang Yaping, wadda ta kasance matukin jirgin saman soja a lokacin, ta fara mafarkinta na zuwa sararin samaniya mai nisa.

'Yar Sama Jannati Da Ke Haskawa A Tashar Sararin Samaniyar Kasar Sin_fororder_Wang Yaping ta tashi a cikin babban akwatin Tianhe

Wang Yaping ta bayyana cewa, lokacin da na kalli kyakkyawar wutar jelar rokar da aka harba, kwatsam sai wani tunani ya fado a cikin zuciyata, muna da 'dan sama jannati na farko a kasar Sin, yaushe ne za mu samu 'yar sama jannati a kasarmu? A wannan lokaci ne, na fara mafarki game da ziyartar sararin samaniya wanda ya dade yana kasancewar a cikin zuciyata. Ni ma ina so in kalli yanayin da sararin samaniya yake, kuma ina so in ba da gudummawa ta dan kadan kan cimma burinmu na Sinawa na zuwa sararin samaniya.

A shekarar 2010, Wang Yaping ta zama daya daga cikin 'yan sama jannati mata na farko na kasar Sin, saboda kwarewar da take da su na tashi sama da kuma kyawawan halaye na tunani. A watan Yuni na shekarar 2013, ta shiga kungiyar kumbon Shenzhou-10 tare da sauran ‘yan sama jannati maza biyu, wato su Nie Haisheng da Zhang Xiaoguang don ziyartar sararin samaniya.

Wang Yaping ta ce, a wannan lokacin, ba na jin wani tsoro a raina, sai dai akwai wasu kalmomi guda shida, wato alhaki, nauyi da kuma cimma mafarki.

A ranar 7 ga watan Nuwamba na shekarar 2021 agogon Beijing, 'yan sama jannatin Shenzhou-13, sun gudanar da ayyukansu na farko na yin zagaye a wajen kumbon. Bayan fita daga kofar kumbon, Wang Yaping ta matsa wajen hannun matakala zuwa wurin gudanar da aikin hadewa don taimakawa Zhai Zhigang wajen hada na'urar dakatar da hannun mutum-mutumi bayan fita daga kunbon. Wang Yaping ya matsa zuwa wajen da za a hade sassan kumbun tare da taimakon Zhai Zhigang don kafa hannun na’urar. Daga baya kuma, ta tsaya kan hannun mutum-mutumi ta yi gwajin motsi na yau da kullun a waje. "Mataki na farko" da 'yar sama jannati ta kasar Sin ta yi ya yi daidai kamar yadda aka tsara.

'Yar Sama Jannati Da Ke Haskawa A Tashar Sararin Samaniyar Kasar Sin_fororder_Wang Yaping ta fita daga kumbon

Kafin Wang Yaping, tun daga shekarar 1984, akwai mata guda 15 a wasu sassan duniya duniya, da suka taba gudanar da ayyukan zagaye a wajen kumbo. A wannan karon, fitowar Wang Yaping ta kuma jawo hankali da kuma samun yabo daga duniya baki daya. Tsohuwar 'yar sama jannati ta NASA Cady Coleman ta rubuta wa Wang Yaping cewa: "Idan kin kalli waje ta tagar, za ki ga manyan taurari, da kasa daga wuri mai nisa, kar ki manta cewa, mata a duniya ma sun kalli wajen tagar ta idanunki, ciki har da ni. "

Irin wannan nasarar da aka cimma, ta kara karfin kasar Sin a fannin bincike sararin samaniya. Game da aikin shigar da 'yan sama jannati mata cikin ayyukan zuwa sararin samaniya, tawagar ayyukan Shenzhou-13 ta yiwa kumbo da tashar sararin samaniya cikakken shiri. Kakakin hukumar kula da sararin samaniyar kasar Sin, kuma mataimakin darektan ofishin injiniyan sararin samaniyar kasar Lin Xiqiang, ya bayyana cewa, tawagar ta Shenzhou-13 ta yi nazari kan halaye na zahiri da bukatu na 'yan sama jannati mata, tare da tsara shirin musamman dake dora muhimmanci kan tabbatar da zaman rayuwa da kiwon lafiya, ta yadda za a ba da tabbaci ga 'yan sama jannati mata, don su saba da yanayin zama da aiki yadda ya kamata a cikin dogon lokaci.