logo

HAUSA

Shugabannin kasashen duniya na taya Sinawa murnar sabuwar shekara

2022-01-31 16:53:52 CMG

Shugabannin kasashen duniya na taya Sinawa murnar sabuwar shekara_fororder_0131-world leaders-Faeza

Shugabannin kasashen duniya sun aike da sakonnin murnar sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin, yayin da Sinawa ke murnar shiga sabuwar shekarar Damisa da za ta kama a gobe Talata.

A sakon da ta aike ta hannun CMG, Firaministar Serbia Ana Brnabic, ta yiwa kasar Sin da al’ummarta, fatan samun nasara da koshin lafiya.

Ta ce Serbia ma na murnar shiga sabuwar shekarar domin bayyana godiyarta ga aminci mai karfi dake tsakaninta da Sin.

Shi ma, Firaministan Cambodia Samdech Techo Hun Sen, ya aike da sakonsa na fatan alkhairi a yau Litinin, yana mai cewa, yanzu bikin na gargajiya ya samu karbuwa a kasarsa dake kudu maso gabashin Asiya.

A nasa sakon taya murnar, Firaministan Japan Fumio Kishida, ya yi Sinawa dake aiki da zama a Japan, tare da daukacin Sinawa fatan alkhairi. Ya kuma yi fatan shekarar za ta kasance mai ban sha’awa dake cike da ci gaba da kuzari. (Fa’iza Mustapha)  

Faeza