Sinawa sun fara shagulgulan murnar bikin bazara mai annashuwa
2022-01-31 20:21:48 CMG
Yau rana ce ta 30 ga wata na 12 bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, kana tun daga yau ne Sinawa suka fara shagulgulan murnar bikin bazara, bikin da ke alamanta shiga wata sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyarsu. A ganina, Sinawa za su ji dadin hutun bikin bazara, musamman ma ganin yadda suka samu tabbaci a wasu fannoni guda 3:
Na farko, an dauki kwararran matakan dakile cutar COVID-19.
Ko da yake ana ci gaba da samun mutane masu kamuwa da cutar COVID-19 a kasar Sin, amma Sinawa ba su damu sosai ba, domin gwamnatin kasar ta dauki kwararran matakai masu amfani wajen hana yaduwar cutar. Misali, yanzu ana samun masu harbuwa da cutar a wasu ungwannin birnin Beijing. Sai dai duk lokacin da aka samu mutanen da suka harbu da cutar, nan take aka killace su a asibiti don jinyar su. A sa’i daya kuma, ana gudanar da bincike kan dimbin mutanen da suka zauna kusa da wadanda suka harbu da cutar. Bisa sakonnin da aka samu a wayar salula, mutane sun san abubuwan da ya kamata su yi. Wasu an yi musu bincike, wasu kuma sun killace kansu a gida. Sauran mutane suna gudanar da harkokinsu yadda suka ga dama, hankalinsu a kwance. Wannan yanayi na samun kwanciyar hankali yana tabbatar da jin dadin bikin da za a yi.
Na biyu, ci gaban tattalin arziki ya sa mutane wadata.
Don biyan bukatun sayen kayayyaki a lokacin biki, ana bukatar samun isashen kudi. Wannan bai zame wa Sinawa matsala ba, ganin yadda kasar ta samu saurin karuwar tattalin arizkin da ya kai kashi 8.1% a shekarar 2021. Wannan karuwa ta tabbatar da ci gaban sana’o’i daban daban na kasar, da samar da karin guraben aikin yi, da karin kudin shiga ga jama’ar kasar. Saboda haka, mutanen kasar sun samu isasshen kudi domin gudanar da sayayya a lokacin bikin, kana gwamnati ita ma ta samu kudin da za tai taimakawa mutanen da suke da bukata. Sanya kowa ya samu isashen kudi don sayen abubuwan da suke bukata, shi ma yana cikin manyan dalilan da suka sa ake murnar biki cikin wani yanayi mai annashuwa a kasar Sin.
Na uku, gudanar da dimbin bukukuwa don kayatar da jama’a.
A Beijing, mutane su kan je wasan kankara a lokacin biki, da kece raini a wasu yankunan wasannin jin dadi, da cin abinci masu dadi a wurare daban daban tare da iyali. Ban da wadannan aikace-aikace, mutane sun samu damar kallon wasu bukukuwa masu kayatarwa. A daren yau, babban gidan rediyo da telabijin na kasar Sin CMG zai watsa wani bikin nune-nune na murnar bikin bazara. Wannan bikin da tarihinsa ya kai shekaru 40, ya kan janyo hankalin mutanen duniya, inda yawan mutanen da su kan kalli bikin ya kan zarta biliyan 1 a kowace shekara. Sa’an nan zuwa ranar 4 ga watan Fabrairu, za a kaddamar da wasannin Olympics na lokacin hunturu a birnin Beijing na kasar Sin. Sinawa a shirye suke, don gudanar da wasannin yadda ake bukata, ta yadda za su burge mutanen duniya, da sanya kowa jin dadinta.
Wadannan fannoni 3 sun ba Sinawa damar jin dadin bikinsu na lokacin bazara. Sai dai mutanen Sin sun cimma nasarar ne bisa kokarin aiki maimakon dogaro kan sa’a. Hakika dukkan ayyukan dakile annoba, da raya tattalin arziki, da karbar bakuncin wasannin Olympics, da gudanar da kasaitaccen biki, suna bukatar shugabancin nagari, da tsari na dogon lokaci, da hadin kai, gami da kokarin gudanar da ayyuka bisa shiri. Wadannan abubuwa sun tabbatar da ci gaban kasar Sin, da nasarorin da ta cimma a fannoni daban daban. (Bello Wang)