logo

HAUSA

‘Yan sama jannati na kasar Sin na shirin gudanar da bikin sabuwar shekarar gargajiya ta Sin a sararin samaniya

2022-01-31 16:56:40 CMG

‘Yan sama jannati na kasar Sin na shirin gudanar da bikin sabuwar shekarar gargajiya ta Sin a sararin samaniya_fororder_0131-saman jannati-Saminu

‘Yan sama jannati na kasar Sin, na shirin gudanar da bikin sabuwar shekarar gargajiya ta Sin a sararin samaniya a karon farko, a gabar da suke daf da cika rabin watanni 6 da aka tsara za su kwashe a samaniya. Yanzu haka dai ‘yan samajannatin, na can a tashar binciken samaniya mallakar kasar Sin, mai nisan kilomita 400 daga doron duniya.

Bikin da ‘yan sama jannatin za su gudanar, na nuna cewa, tawagar mai aiki a kumbon Shenzhou-13, ba za ta jingine al’adar Sinawa ta gudanar da bikin na sabuwar shekara ba, inda suke ci gaba da shirye shiryen gudanar da shagulgula a samaniya.

Wani faifan bidiyo da CMG ya fitar, ya nuna yadda ‘yan samajannatin ke kawata cikin tashar binciken samaniyar da balanbalan, da takardu masu launin ja, dake dauke da kalmar fatan alheri, wadda ke nuni ga zuwan lokacin farin ciki.

Zhai Zhigang, daya daga ‘yan samajannatin, ya yi amfani da wani burushin fenti wajen rubuta wasu haruffa a gaban kyamara, masu dauke da sakon fatan alheri na zuwan wannan sabuwar shekara, inda ya rubuta "Barkan ku da zuwan sabuwar shekarar, da fatan koshin lafiya da dukkanin sa’a a wannan shekara ta Damisa!"  (Saminu)

Saminu