logo

HAUSA

Wani harin ‘yan bindiga a arewacin Nijeriya ya yi sandin rayuka 11

2022-01-31 16:58:16 CMG

Wani harin ‘yan bindiga a arewacin Nijeriya ya yi sandin rayuka 11_fororder_0131-Nigeria-Faeza

Mutane a kalla 11 sun mutu, biyo bayan wani hari da ‘yan bindigar da ba a san ko su wanene ba, suka kai jihar Kaduna dake arewacin Nijeriya.

Kwamishinan kula da tsaro da al’amuran cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, wasu ‘yan bindiga sun kai hari wani kauye dake yankin karamar hukumar Zango Kataf da safiyar jiya Lahadi.

Ya kara da cewa, an kona gidaje 30 yayin harin. Kana an kai wasu da suka jikkata zuwa asibiti, yana mai cewa, ana ci gaba da aikin bincike da ceto da kuma farautar maharan.

Arewacin Nijeriya dai na fama da hare-haren ‘yan bindiga a baya-bayan nan, baya ga satar dabbobi da fashi da makami. (Fa’iza Mustapha)

Faeza