Sabiqu Shareef Ahmed: Ina matukar sha’awar yaren Sin da al’adun Sinawa
2022-02-01 14:04:12 CRI
Sabiqu Shareef Ahmed, mazauni ne dake jihar Kano a arewacin Najeriya, wanda ya dade yana sauraron shirye-shiryen sashen Hausa na rediyon kasar Sin wato CRI Hausa.
A zantawarsa da Murtala Zhang, Shareef ya bayyana tarihinsa na koyon harshen Sinanci, da yadda yake fahimtar al’adu gami da halayen Sinawa.
Shareef ya kuma yi kira ga mutanen Najeriya su tantance gaskiyar labaran da wasu kafafen yada labaran kasashen yammacin duniya ke yadawa game da kasar Sin, inda a cewarsa, akasarin labaran da suke yadawa, karya ce ko jita-jita don shafawa gwamnatin kasar Sin bakin fenti. (Murtala Zhang)