logo

HAUSA

Shugaban Zimbabwe na da yakinin cewa gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi a Beijing zai gudana cikin nasara

2022-01-29 16:50:59 CRI

Shugaban Zimbabwe na da yakinin cewa gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi a Beijing zai gudana cikin nasara_fororder___172.100.100.3_temp_9500033_1_9500033_1_1_2eae6c33-2e4f-480c-922f-b1680d3aafa9 快捷方式

A yayin da yake zantawa da ‘yan jaridun babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, shugaban kasar Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa ya ce, gasar wasannin motsa jiki na Olympics da aka shirya a Beijing a shekara ta 2008, ta shaidawa daukacin duniya kwarewar Beijing wajen gudanar da gagarumar gasa. Ya ce a halin yanzu, kasa da kasa na sa ran gudanar da gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi a Beijing cikin nasara, inda kuma suke da yakinin cewa gasar za ta zama kasaitacciya. Mnangagwa ya ce:

“Kasar Sin za ta karbi bakuncin gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu a Beijing a wata mai zuwa. Ina wa al’umma gami da gwamnatin kasar Sin fatan alheri, da kuma fatan gudanar da gasar cikin gagarumar nasara. Ina da yakinin cewa gasar ta bana za ta zama mai burgewa kamar irin ta shekara ta 2008. Na yi imanin cewa, ‘yan wasannin motsa jiki suna alla-alla su halarci gasar a Beijing. Ina wa gasar fatan alheri.”

Sakamakon bambancin yanayin wurare, ‘yan wasannin motsa jikin Zimbabwe ba su kware a fannin wasannin lokacin sanyi ba, don haka, babu wanda zai halarci gasar a Beijing a bana. Amma kasar ta taba samun babbar nasara a gasar wasannin Olympics na lokacin zafi na Beijing a shekara ta 2008, inda ‘yar wasan ninkaya Kirsty Coventry ta lashe lambobin yabo har guda hudu, al’amarin da ya zama tarihi a Zimbabwe. (Murtala Zhang)