logo

HAUSA

Majalisar dokokin Ghana zata bincike musababbin fitar da Black Stars daga wasannin AFCON

2022-01-29 17:17:41 CRI

Majalisar dokokin Ghana zata bincike musababbin fitar da Black Stars daga wasannin AFCON_fororder_VCG111365503956

Majalisar dokokin kasar Ghana, ta kafa wani kwamiti a jiya Juma’a, domin bincike game da saurin fitar da kungiyar kwallon kafa ta Black Stars ta kasar, daga wasannin cin kofin Afrika dake gudana a Kamaru.

Mataimaki na farko na shugaban majalisar dokokin kasar Joseph Osei-Wusu, ya umarci kwamitin ya gudanar da bincike domin gano musabbabin rashin tabuka abun kirki daga ‘yan wasan Black Stars, tare da mikawa majalisar rahotonsa.

Zuwa yanzu, kasar Ghana ta halarci gasar AFCON har sau 23, tun bayan da aka kaddamar da gasar a shekarar 1957.

A bana, maki daya kadai Black Stars din ta samu daga cikin 9, bayan kunnen doki na ci 1-1 a wasan da ta buga da Gabon, da kuma rashin nasara da ci 1-0 a wasanta da Morocco, sai kuma ci 3-1 a wasanta da Comoros, lamarin da ya kai ga fitar da kungiyar, wadda ta taba lashe gasar har sau 4. Wannan dai, ita ce wasa mafi muni a tarihin kasar.

Gwamnatin kasar Ghana ta bayyana wasan Black Stars a matsayin mara kyau, inda ta bada shawarar sallamar kocin kungiyar Milovan Rajevac. (Fa’iza Mustapha)