logo

HAUSA

Shugaban kwamitin shirya wasannin Olympics na Nijeriya: Na san Beijing ta shirya

2022-01-29 20:26:34 CRI

Shugaban kwamitin shirya wasannin Olympics na Nijeriya: Na san Beijing ta shirya_fororder_db9e-irpunai1567947

Shugaban kwamitin shirya wasannin Olympics na Nijeriya, Habu Ahmad Gumel, ya ce gudanar da wasannin Olympics na lokacin hunturu na Beijing ba tare da wata tangarda ba yayin da ake fama da annobar COVID-19, yana da matukar muhimmanci wajen karfafa abota da hadin kai tsakanin kasashe, yana mai cewa, ya san komai ya riga ya kankama a Beijing.

Habu Ahmad Gumel, wanda kuma mamba ne na kwamitin shirya wasannin Olympics na kasa da kasa,ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da wakiliyarmu, inda ya ce COVID-19 ta yi mummunan tasiri ga dukkan kasashe, ciki har da Nijeriya. Amma duk da haka, zai halarci wasannin na Beijing daga Nijeriya. Ya kuma bayyana yakini game da matakan kandagarkin cutar da aka dauka a Beijing.

Har ila yau, Habu Gumel ya ce wannan ne karo na 2 da Nijeriya ta tura tawaga zuwa wasannin Olympics na lokacin hunturu, kuma samun gayyata daga kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa na da muhimmanci gaya ga‘yan wasan kasar. Yana mai fatan wasannin na Beijing, za su gudana cikin nasara. (Fa’iza Mustapha)