logo

HAUSA

Mutane miliyan 15 a tsakiyar Sahel za su bukaci agaji a shekarar 2022

2022-01-28 11:28:12 cri

Mutane miliyan 15 a tsakiyar Sahel za su bukaci agaji a shekarar 2022_fororder_0128-Sahel-Ahmad

Sakamakon yawaitar tashe tashen hankula a tsakiyar yankin Sahel, ana fargabar mutane miliyan 15 za su bukaci tallafin jinkai a shiyyar cikin wannan shekara ta 2022, Martin Griffiths, babban jami’in sashen agajin gaggawa na MDD ya bayyana hakan.

Ya ce, matsalar sauyin yanayi, da karuwar rikice-rikicen siyasa, da karancin damammakin ci gaba mai dorewa, da karuwar talauci, da yaduwar annobar COVID-19 a kasashen Burkina Faso, Mali da Nijer, su ne manyan matsalolin dake barazana ga shiyyar. Mutane miliyan 15 za su bukaci tallafin a bana adadin da ya karu da sama da mutane miliyan 4 idan an kwatanta da wadanda suka bukaci tallafin a shekarar bara.

Ya kara da cewa, hakan na nufin cewa, a shekarar 2022, za a bukaci kusan dala biliyan biyu domin aiwatar da ayyukan jinkan bil adama a wadannan kasashen uku.

Jami’in agajin gaggawar ya gabatar da jawabi ne a taron tattaunawa ta kafar bidiyo game da batun dake shafar yankin tsakiyar Sahel, bayan ziyarar da ya kai zuwa arewa maso gabashin Najeriya a makon jiya dake makwabtaka da shiyyar.

Griffiths ya bukaci a mayar da hankali kan tabbatar da sauye-sauye, da dawwamammiyar hanyar warware matsaloli, da hadin gwiwar dukkan fannonin, don samar da agajin jin kan bil adama da samar da ci gaba da kokarin tabbatar da zaman lafiya da hakikanin cigaba. (Ahmad Fagam)