logo

HAUSA

Sharhi: Wadannan alkaluma sun nuna ikirarin warewa maganar fatar baki ce kawai

2022-01-28 14:08:46 CRI

Sharhi: Wadannan alkaluma sun nuna ikirarin warewa maganar fatar baki ce kawai_fororder_0128-Ahmad-sharhi-

Idan an dubi alkaluman yadda cinikayya da zuba jari a sassan duniya ke gudana cikin ’yan shekarun baya bayan nan, za a gane cewa, duk wani yunkuri na warewa daga kasar Sin ba zai haifar da ‘da mai ido’ ba.

Wasu alkaluma da bayanai na baya bayan nan da kasar Sin ta fitar a bara, game da tattalin arzikin kasar, da kuma sakamakon jerin nasarorin da kasar ta samu karkashin hadakarta da sassan kasa da kasa, sun sake jaddada wannan lamari.

Duniya na bukatar kasar Sin. Kuma Sin a nata bangaren wadda ake kallo a matsayin "Babbar masana’antar duniya", ta na da karfin ikon samar da hajoji, ta yadda ta zama jigo wajen daidaita samar da hajojin da duniya ke bukata. Alkaluman shekarar bara da hukumar Kwastam ta kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, darajar cinikayyar Sin da Amurka ta kai dalar Amurka biliyan 755.645, wato karuwar kaso 28.7 bisa dari a shekara guda, wanda kuma hakan ya nuna sabon matsayi na ci gaba da aka samu a wannan fanni.

Wannan dai na kara nuni da yadda kasashen biyu ke dogaro da juna a fannin raya tattalin arziki da cinikayya. Kuma duk wani furuci na nuna rabuwa tsakanin Sin da Amurka zance ne maras ma’ana.

Kaza lika, ita ma Sin na bukatar sauran sassan duniya. Duba da cewa, ci gaban tattalin arzikin duniya cikin gwamman shekarun da suka gabata, ya hade wuri guda, zuwa yanayi na tsarin tattalin arzikin duniya a dunkule. Sauye sauye da kara bude kofa sun ingiza ci gaba a Sin, tare da samarwa Sinawa kyakkyawar rayuwa. Wannan ma wani muhimmin dalili ne da ya sanya Sin ta jima tana goyon bayan cudanyar dukkanin sassa, da dunkulewar duniya baki daya. Sin za ta samu zarafin kara bunkasa ne kawai, idan ragowar sassan duniya suka samu nasarar bunkasuwa, ta yadda dukkanin duniya za ta bunkasa.   (Saminu)