logo

HAUSA

An gudanar da kayetaccen bikin sabuwar shekarar Sinawa a Najeriya

2022-01-28 14:21:57 CRI

An gudanar da kayetaccen bikin sabuwar shekarar Sinawa a Najeriya_fororder_0128-Nigeria-Ahmad

Jiya Alhamis, al’ummar Sinawa mazauna Najeriya sun shirya kasaitaccen bikin murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargaiyar Sinawa ta Damisa wacce ke shirin kamawa.

Bikin, an gudanar dashi a ofishin jakadancin kasar Sin dake Najeriya, ya samu halartar dandazon Sinawa mazauna kasar, da jami’an gwamnatin Najeriya, da kuma dalibai.

Mahalarta bikin, sun taru a cibiyar raya al’adun gargajiyar kasar Sin dake tsakiyar birnin tarayya Abuja, inda suka nishadantu da wasannin gargajiyar kasar Sin daban daban, da suka hada raye rayen gargajiyar kasar Sin na dragon da na zaki.

Jakadan kasar Sin a Najeriya, Cui Jianchun, ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, bikin ya kasance a matsayin wani mafari ne na kyawawan abubuwa, kamar nuna kwarin gwiwa, da jarumta, da burika.

Bikin bazarar Sinawa yana kara samun karbuwa a biranen Najeriya da dama sakamakon kyakkyawan fata da kuma kaunar da alummun Sinawa suke nunawa kasar mafi yawan alumma a nahiyar Afrika. (Ahmad)