logo

HAUSA

Karon farko yawan kudin cinikayyar kayayyaki tsakanin Sin da Rasha a shekarar 2021 ya zarce dala biliyan 140

2022-01-28 11:16:37 CRI

Karon farko yawan kudin cinikayyar kayayyaki tsakanin Sin da Rasha a shekarar 2021 ya zarce dala biliyan 140_fororder_src=http___p4.itc.cn_q_70_images03_20210906_f467003ffa574de78e6dc83542fc5210.jpeg&refer=http___p4.itc

Ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta ba da kididdiga a jiya Alhamis cewa, a shekarar 2021 hadin kan Sin da Rasha a fannin tattalin arziki da cinikayya ya samu ci gaba mai armashi, inda yawan kudin dake shafar cinikin kayayyaki tsakaninsu ya kai dala biliyan 146.87, wanda ya karu da kashi 35.9% bisa na makamancin lokaci na shekarar 2020, hakan ya sa kasar Sin ta zama abokiya mafi karfi ga Rasha ta fuskar ciniki a cikin shekaru 12 a jere.

A shekerar bara, kasashen biyu sun samu sabon ci gaba kan wasu manyan ayyuka. Ciki har da sanya hannu a takardar yarjejeniyar fahimtar juna kan gina tashar nazarin duniyar wata ta kasa da kasa, da taswirar tauraron Bil Adama masu ba da jagoranci, da makamashin gas, da masana’antun hada sinadari, da kera na’urorin zirga-zirga a sararin samaniya da sauransu. Mai magana da yawun ma’aikatar Gao Feng ya nuna cewa:

“Ma’aikatar da bangaren Rasha sun kammala aikin tsara taswirar bunkasa sha’anin cinikin kayayyaki da ba da hidima, da kuma sa hannu kan takardar fahimtar juna ta fuskar tattalin arziki na yanar gizo da zuba jari. Ban da wannan kuma, bangarorin biyu sun kulla yarjejeniyar fahimtar juna wajen raya tattalin arzikin yanki tsakanin bangarori daban-daban, ta yadda za a kara hadin kansu da yin sulhu a kungiyoyin WHO da BRICS da SCO da sauransu, da ingiza raya shawarar ‘ziri daya da hanya daya’ da kungiyar hadin kan Euro da Asiya kan tattalin arziki.” (Amina Xu)