logo

HAUSA

Kasar Mali ta karbi sabon rukunin alluran rigakafin COVID-19 da kasar Sin ta samar mata

2022-01-28 20:13:45 CRI

Kasar Mali ta karbi sabon rukunin alluran rigakafin COVID-19 da kasar Sin ta samar mata_fororder_微信图片_20220128201258

A ranar Laraba ne wani sabon rukunin alluran riga kafin COVID-19 da kasar Sin ta baiwa kasar Mali, suka isa Bamako babban birnin kasar

Jakadan kasar Sin dake kasar Mali Chen Zhihong, da ministar lafiya da raya zamantakewar al’umma ta kasar Mali Dieminatou Sangare, sun halarci bikin da aka shirya a filin jirgin saman kasa da kasa dake Bamako.

A jawabinta Sangare ta bayyana godiyarta ga gwamnatin kasar Sin a madadin shugaban rikon kwarya na kasar Mali Assimi Goita, da gwamnatin rikon kwarya da kuma al'ummar kasar Mali. Ta ce, a ko da yaushe kasar Sin tana taimakawa 'yan kasar Mali, kuma kasar Mali a shirye ta ke ta ci gaba da zurfafa hadin gwiwa da kasar Sin.

Ta kara da cewa, kasar Sin ta baiwa kasar Mali kayayyakin yaki da annobar da dama, wadanda suka taimakawa Mali matuka a yaki da cutar, kuma halin da ake ciki a kasar Mali, ya tabbatar da cewa, allurar riga kafi na kasar Sin na da inganci kuma abin dogaro ne.