logo

HAUSA

Ta yaya harkar binciken sararin samaniya ta kasar Sin za ta kirkiro makoma mai kyau ga dan Adam?

2022-01-28 21:20:45 CRI

Ta yaya harkar binciken sararin samaniya ta kasar Sin za ta kirkiro makoma mai kyau ga dan Adam?_fororder_微信图片_20220128211933

A ranar 1 ga watan Janairun bana, wani marubuci kan ilimin binciken sararin samaniya na kasar Sifaniya, Pedro Leon ya bayyana cewa, yana ji kamar kasar Sin tana cikin shekara ta 2122. Pedro ya yi wannan furuci ne bayan da ya ga ingantattun hotunan da hukumar binciken sararin samaniyar kasar Sin ta wallafa, wadanda na’urar binciken duniyar Mars da ta harba mai suna Tianwen-1 ta aiko.

Menene sirrin ci gaban harkokin binciken sararin samaniyar kasar Sin? Wane buri kasar take kokarin cimmawa a wannan fanni? Wata takardar bayani mai suna “harkokin sararin samaniya na kasar Sin na shekara ta 2021” da aka wallafa yau Jumma’a ta bada amsa.

Wannan ita ce takardar bayani ta biyar da kasar Sin ta fitar a tarihi dangane da harkokinta na binciken sararin samaniya, inda aka takaita nasarorin da kasar ta samu a fannoni 11 cikin shekaru 5 da suka wuce, da kafa muhimmiyar alkibla ga harkokin binciken sararin samaniya na kasar Sin nan da shekaru 5 masu kamawa. Abun lura a nan shi ne, a karo na farko takardar ta bayyana cewa, ya dace a gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya a sararin samaniya.

Nan da shekaru biyar masu zuwa ko ma a nan gaba fiye da haka, duniya za ta kalli yadda kasar Sin take bude kofarta da habaka hadin-gwiwa da more nasarori tare da sauran kasashe a fannin binciken sararin samaniya, da yadda take kara samar da alheri da ci gaba ga daukacin al’umma. (Murtala Zhang)