logo

HAUSA

UNECA: nasarar fitar da gahawar kasar Habasha zuwa Sin abun a yaba ne

2022-01-28 14:06:26 CRI

UNECA: nasarar fitar da gahawar kasar Habasha zuwa Sin abun a yaba ne_fororder_0128-UNECA-Saminu

Babbar jami’ar hukumar raya tattalin arzikin Afirka ta MDD Vera Songwe, ta jinjinawa nasarar da aka cimma game da fitar da Gahawar kasar Habasha zuwa kasar Sin, matakin da a cewar jami’ar, zai share fagen fitar da karin hajojin kasashen Afirka zuwa ketare.

Babbar jami’ar hukumar ta UNECA, wadda ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kwafin ta, ta ce hukumar na farin cikin nasarar aikin da ta yi tare da mahukuntan Habasha, wajen amfana daga wannan dama, tana kuma fatan wannan hadin gwiwa zai ci gaba da inganta rayuwar al’ummun Habasha, ta hanyar gabatar da karin damammakin cinikayya gare su.

A cewar hukumar UNECA, sama da buhunan Gahawa 11,200 kasar Habasha ta sayar cikin ’yan dakikoki a makon da ya gabata, lokacin kaddamar da samfurin Gahawar kasar kan manhajar sayayya ta yanar gizo ta Alibaba, wato “Tmall Global”, karkashin hadin gwiwar hukumar ECA da gwamnatin Habasha.

Da yake tsokaci kan hakan, ministan ma’aikatar cinikayyar kasa da dunkulewar shiyya na kasar Habasha Gebremeskel Chala, ya ce wannan kaddamarwa, ta nuna alfanun dake tattare da ci gaban, ba ga kasar Habasha kadai ba, har ma da sauran sassan kasashen Afirka, duba da yadda zai ba da damar cin gajiya daga kasuwanci ta yanar gizo. (Saminu)