logo

HAUSA

Sin ta fitar da takardar bayani game da shirinta na binciken sararin samaniya

2022-01-28 14:24:28 CRI

Sin ta fitar da takardar bayani game da shirinta na binciken sararin samaniya_fororder_0128-white paper -Saminu

A Juma’ar nan ne, kasar Sin ta fitar da takardar bayani game da shirinta na binciken sararin samaniya. Takardar bayanin mai taken "Shirin binciken samaniya na Sin: Makomarsa a 2021" na kunshe da gabatarwa game da dalilan Sin, da ka’idojin ayyukanta, da manufofi da matakai, da fatanta na hadin gwiwa a ayyukan binciken sararin samaniya. Kaza lika ta yi bitar nasarorin da kasar ta samu a kimiyyar sararin samaniya, da fasahohin sararin samaniya, da alfanun da Sin din ta samu daga ayyukan.

Manyan nasarori da Sin ta cimma a wannan fanni tun daga shekarar 2016, sun hada da wanzuwar nasarori a fannin kayayyakin aiki, da kammalawa, da fara aikin tsarin tauraron dan Adam na BeiDou mai ba da hidimar taswira, da kammala tsarin daukar hotunan sassan duniya mai inganci, da kara daidaita ayyukan taurarin dan Adam masu ba da hidimar sadarwa, da watsa shirye shirye, da kammala matakin karshe cikin matakai 3 na nazarin duniyar wata. Matakin farko shi ne na gina cibiyar binciken samaniya ta Sin, da saukar tauraron Tianwen-1, da kuma binciken duniyar Mars, kamar dai yadda takardar bayanin ta fayyace.

Har ila yau, wannan takarda, ta bayyana aniyar kasar Sin game da kara azama, wajen binciken yankunan duniyar wata, da fatan saukar bil Adama a duniyar wata.

A daya hannun kuma, takarda ta ce Sin na kira ga sauran kasashen duniya, da su yi musaya mai zurfi, da hadin gwiwa a ayyukan binciken sararin samaniya bisa daidaito, da cin gajiyar juna, da cimma gajiya cikin lumana, da bunkasuwa daga dukkanin fannoni.

Sin na fatan samun karin hadin gwiwa a ayyukan sama jannati, da horaswa, da hadin gwiwar harba kumbuna, da sauran fannoni da Sin din za ta iya yin hadin kai da sauran kasashen waje. Bugu da kari, Sin za ta karfafa hadin gwiwa a fannin kafa cibiyar binciken duniyar wata ta kasa da kasa.   (Saminu)