logo

HAUSA

Kungiyoyin kwallon kafar kasashe 8 sun kai zagaye na gaba a gasar cin kofin Afirka

2022-01-27 11:26:51 CRI

Daga ranar 23 zuwa 26 ga wata, an buga wasannin zagaye na 2, inda kungiyoyin kwallon kafar kasashe 8 suka kai zagaye na gaba a gasar cin kofin Afirka dake gudana yanzu haka a kasar Kamaru.

Kungiyoyin kasashen Masar, da Kamaru, da Morocco, da Tunisiya, Burkina Faso, da Sanegal, da Gambiya, da Equatorial Guinea ne suka kai zagayen gasar na gaba.

Za a buga wasannin gaba tun daga ranar 29 da 30 ga wata, inda za a kara tsakanin Gambiya da Kamaru, da tsakanin Masar da Morocco, da tsakanin Burkina Faso da Tunisiya, da kuma tsakanin Senegal da Equatorial Guinea. (Kande Gao)