logo

HAUSA

UNICEF ta kaddamar da gangamin wayar da kai game da muhimmancin rigakafin COVID-19 a Afirka

2022-01-27 10:38:27 CRI

UNICEF ta kaddamar da gangamin wayar da kai game da muhimmancin rigakafin COVID-19 a Afirka_fororder_220127-saminu-UNICEF

A jiya Laraba, asusun yara na MDD UNICEF, ya kaddamar da gangamin wayar da kai na makwanni 8, domin wayar da kan al’umma game da muhimmancin karbar rigakafin cutar COVID-19 a sassan nahiyar Afirka.

Wani rahoto da abokan huldar UNICEF suka fitar mako guda, bayan gabatar da rigakafin cutar COVID-19 na biliyan guda ga kasar Rwanda, karkashin shirin COVAX, ya ja hankalin abokan huldar asusun su miliyan 13.3, dake sassan Afirka daban daban, game da bukatar yayata muhimmancin yiwa karin mutane rigakafin.

A cewar UNICEF, tuni aka riga aka aike da sakwannin wayar da kai game da annobar COVID-19 ta hanyar gajerun sakwannin Facebook da sauran su, domin amfanin al’ummun nahiyar.

UNICEF ta ce ganganin wayar da kan na makwanni 8, wanda aka yiwa take da “Gwada kwazo" zai gudana ne a kasashen Afirka 6, da suka hada da Kwadebuwa, da Ghana, da Kenya, da Najeriya, da Afirka ta kudu, da Zimbabwe.   (Saminu)