logo

HAUSA

Juma’ar da za ta yi kyau tun daga Laraba ake gane ta

2022-01-27 16:17:31 cri

Juma’ar da za ta yi kyau tun daga Laraba ake gane ta_fororder_sharhi

Yanzu haka kasa da makwanni 2 suka rage a bude gasar Olympics ta lokacin hunturu da birnin Beijing zai karbi bakunci, inda kuma hankulan duniya ke kara karkata ga wannan kasaitacciyar gasa ta kasa da kasa, wadda kasar Sin ke fatan gudanarwa, duk da tarin kalubale da duniya ke fuskanta, musamman ma batun ci gaba da bazuwar annobar COVID-19 a sassan duniya, da ma yadda wasu sassa ke kokarin siyasantar da batun wasanni.

Wani abun lura a nan shi ne, duk da tarin kalubalen da ake hange, masharhanta da dama na da karfin gwiwar kammalar wannan gasa cikin nasara, duba da yadda kasar Sin ta yi namijin kokarin kimtsawa yadda ya kamata.

Jami’ai daga hukumomin shirya wasanni na kasa da kasa, ciki har da kwamitin shirya gasar Olympics na kasa da kasa IOC, sun jinjinawa kwazon Sin a fannin kyautata wuraren gudanar da gasar, wanda hakan ya ingiza goyon baya da amincewar sassan kasa da kasa da shirin na kasar Sin.

Bahaushe kan ce “Juma’ar da za ta yi kyau tun daga Laraba ake gane ta”. Ga duk mai bibiyar tsare tsare da Sin ta gudanar domin karbar bakuncin wannan gasa cikin nasara, zai amince da nagartar tanadin da aka yi mata, kama daga samar da fasahohin zamani na kare lafiyar mahalartan ta, zuwa amfani da abubuwan da za su kare muhalli. Kaza lika an tanaji kwararrun masu aikin sa kai, da tawagar jami’an lafiya da jami’an tsaro isassu.

Sabanin yadda wasu ke tunani, a wannan karo, akwai kasashe da dama da suka aiko da wakilan su karkashin tawagar kasashen su, domin halartar wannan gasa ta Olympics a karo na farko a tarihin su. Kuma duk da matsalolin da duniya ke fuskanta, gasar Olympics ta hunturu ta birnin Beijing na maraba da ’yan wasa kimanin 3,000, daga kasashe da yankuna 90, wadanda za su fafata neman lashe lambobin yabo mafiya yawa da aka taba tsara bayarwa ga ’yan wasa a tarihin gasar Olympics ta lokacin hunturu.

Masu fashin baki da dama dai na jinjinawa kasar Sin, sakamakon yadda ta tanaji wani tsarin musamman, mai kunshe da fasahohin zamani, da na’urori daban daban, wadanda za su taimaka wajen kaucewa yaduwar annobar COVID-19 mai saurin bazuwa. Wannan mataki na kan gaba, wajen karfafa gwiwar dukkanin sassa, game da yiwuwar gudanar da gasar Olympics mai matukar kayatarwa. (Saminu Hassan)