logo

HAUSA

Tanzania ta karbi karin tallafin rigakafin COVID-19 daga kasar Sin

2022-01-27 10:01:02 CRI

Tanzania ta karbi karin tallafin rigakafin COVID-19 daga kasar Sin_fororder_220127-Saminu-Tanzania

A ranar Laraba ne kasar Tanzania ta karbi karin tallafin rigakafin cutar COVID-19 na kamfanin Sinopharm har 800,000, wanda ya kasance karo na biyu da kasar ke samun irin wannan tallafi daga kasar Sin.

Jakadiyar Sin a kasar Chen Mingjian ce ta mika rigakafin ga ministar lafiya, raya al’umma, kula da tsoffi da kananan yara ta kasar Ummy Mwalimu, a filin jirgin saman kasa da kasa na Julius Nyerere dake birnin Dar es Salaam.

Da take tsokaci yayin karbar rigakafin, minista Ummy Mwalimu, ta ce rigakafin 800,000 da kasarta ta samu a wannan lokaci, za ta isa a yiwa mutum 400,000 cikakkun rigakafi, yayin da tuni kason farko na alluran rigakafin 500,000 da kasar Sin ta tallafawa kasar da su a watan Nuwambar bara, aka yi amfani da su wajen yiwa mutum 250,000 cikakken rigakafin cutar.

A nata bangare kuwa, Chen cewa ta yi Sin ta riga ta mika kason farko na rigakafin guda 500,000 samfurin kamfanin Sinopharm ga Tanzania, kuma a nan gaba kadan, Sin za ta baiwa kasar karin alluran rigakafi miliyan 1 na kamfanin Sinovac.   (Saminu)