logo

HAUSA

Xi ya jaddada zamanantar da yankunan karkara

2022-01-27 21:13:22 CRI

Xi ya jaddada zamanantar da yankunan karkara_fororder_f44d305ea4db235c980c22

Babban sakataren kwamitin koli na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada muhimmancin zamanantar da aikin gona da yankunan karkara, a daidai gabar da kasar Sin ke kokarin gina kasa mai bin salon gurguzu ta zamani a dukkan matakai.

Xi ya bayyana haka ne a jiya Laraba, yayin da ya ziyarci wani kauye da ke gundumar Fenxi da ke lardin Shanxi na arewacin kasar Sin.

Shugaba Xi ya ce, abin farin ciki ne ganin yadda mazauna kauyen suka gamsu da yadda suke rayuwa.

Ya kuma lura da cewa, akwai sauran rina a kaba, kafin cimma burin kasar Sin mai bin tsarin gurguzu ta zamani. A don haka, Xi ya bukaci a kara karfafa nasarorin da aka cimma na kawar da talauci, da ciyar da yankunan karkara gaba, da kuma zamanantar da rayuwar karkara.