Kocin kungiyar kwallon kafar Zimbabwe yana taimakawa karin yara wajen cimma burinsu kan wasan
2022-01-27 16:13:08 CRI
Domin begen zuwa kasar Sin, wasu ‘yan kasashen waje sun tashi daga kasashensu zuwa kasar Sin, don neman cimma burinsu, kana sun zabi ci gaba da yin rayuwa a kasar Sin. Walter Musanhu, dan kasar Zimbabwe yana daya daga cikinsu.
A shekarar 2016, Walter Musanhu, ya tashi daga kasarsa ta Zimbabwe zuwa kasar Sin, ya zuwa yanzu, ya riga ya koyar da fasahohin wasan kwallon kafa har na tsawon shekaru fiye da 5 a kasar Sin. Kana ya kusan cika shekaru 3 da kafa makarantarsa ta koyar da wasan kwallon kafa. Lokacin da ya zo kasar Sin, ya yi aiki a kamfanin wasu mutane, kana a zuwa ya kafa kamfanin sa, inda makarantar da ya kafa ta karbi yara daga uku kawai da farko zuwa kimanin dari daya a yanzu, wannan dan kasar Zimbabwe ya samu nasara, da farin ciki sosai kan rayuwarsa ta neman cimma burinsu a kasar Sin.
A wata ranar Asabar ta karshen watan Disamba na shekarar 2021, a wani filin wasan kwallon kafa dake wurin yawon shakatawa na Side na birnin Beijing, aka yi gasar wasan kwallon kafa ta sada zumunta a tsakanin rukunonin biyu na yara masu shekaru 8 ko 9. A gefen filin wasan, Walter Musanhu yana sa ido sosai kan wasu yaran da suke buga kwallon kafa a gun gasar.
An haifi Walter Musanhu a shekarar 1987, ya zo daga kasar Zimbabwe, wanda ya taba zama dan wasan kwallon kafa a kasar, kana ya taba buga wasan kwallon kafa a gasar wasan kwallon kafa a kasar Austria. Amma bayan da ya ji rauni, ya bar nahiyar Turai da koma kasarsa ta Zimbabwe, saidai ya yi ritaya daga dandalin buga wasan kwallon kafa. Bayan hakan, ya samu takardar izinin zama mai horaswa na wasan kwallon kafa ta Turai da ta Afirka, kuma a shekarar 2016, ya zo kasar Sin.“Tun daga shekarar 2016 zuwa 2019, na zama mai horaswa a wata kungiyar koyar da fasahohin wasan kwallon kafa a kasar Sin.”
Bayan da ya zo kasar Sin, Walter ya zama mai horaswa na wasan kwallon kafa ga matasa da yara. Bayan da ya samu wasu fasahohin tafiyar da kamfanin koyar da fasahohin wasan kwallon kafa, a karshen rabin shekarar 2019, Walter ya bude kamfaninsa na koyar da wasan kwallon kafa, wato makarantar wasan kwallon kafa ta JADEL FA. Walter ya bayyana cewa,“Ga wani mutum daga kasar waje, na fuskanci kalubale da dama wajen kafa kamfani na. Abu mafi wuya shi ne bayan da na kafa kamfanin da farko, yaya za a jawo karin dalibai su zo makaranta tawa.”
A ganin iyayen daliban da suke koyon fasahohin wasan kwallon kafa, Walter yana da halaye masu kyau, da koyar da yara fasahohin wasan kwallon kafa mai kyau, da kuma maida hankali sosai ga yanayin yara. Wasu yara sun shiga makarantar Walter tun kafa ta, sun zabi Walter a matsayin mai horaswar su musamman. Kana iyayen yaran da suke koyon wasan a makarantar Walter suna amince da tunani, da hanyoyinsa na koyar da fasahohin wasan. Iyayen sun bayyana cewa,“Yaro na ya kalli horaswar da malam Walter ya yi a kos, daga nan ya gaya mini yana son shiga kos din, bayan da ya yi kos sau daya kacal, sai ya gaya mini cewa yana son buga wasan kwallon kafa tare da malam Walter, kuma har yanzu yana kiyaye yin kos tare da shi.”
“Domin tunaninsa na koyar da fasahohin wasan kwallon kafa yana da kyau, na amince da shi, wato yin wasan don kiwon lafiya da kuma horaswa da yin hadin gwiwa a tsakanin yara.”
“Ko sabbin dalibai ko tsofaffin dalibai a makaranta, zai iya samar musu damar shiga gasar wasan cikin adalci.”
A ganin Walter, yaran kasar Sin suna kaunar wasan kwallon kafa, ya ce idan aka samu hanya mai dacewa, yana iya yin mu’amala mai kyau tare da su. Walter ya ce,“Ina yin amfani da hanyar musamman yayin da nake yin mu’amala da yara. Ina gaya wa yara su zama cikin yanayin yarintar su, kana ni zan fahimce su a matsayin yara. Za mu fahimci juna. Halin zuciyar yara ba shi da sarkakkiya, suna bukatar kauna da kulawa, lokacin da muke nuna musu kauna da kulawa, muna kafa dangantaka mai kyau. Don haka, lokacin da sabbin dalibai suka zo makaranta, zan sa su yi abin da suke son yi, zan gano ra’ayoyinsu, babu shakka ta hakan za su fahimce ni.”
An haifi Walter a unguwar matalauta ta Mbare dake birnin Harare na kasar Zimbabwe. Domin yin wasan kwallon kafa, Walter ya samu damar fito daga unguwar, kana ya yi kokari wajen raya sha’aninsa da kafa kamfani. Walter yana fatan yara masu kaunar wasan kwallon kafa kamar shi, za su cimma burinsu da yin rayuwa mai ban sha’awa. Walter yana da shirin jagorantar dalibansa na kasar Sin, zuwa kasarsa ta Zimbabwe bayan wucewar yaduwar cutar COVID-19, don ganin wurin da ya yi rayuwa a lokacin kuruciyarsa da idanunsu. Walter ya bayyana cewa,“Idan komai ya tafi yadda ya kamata, ina son bude wani aikin mu’amalar al’adu a tsakanin kasar Zimbabwe da kasar Sin, don samar da dama ga yaran kasar Sin su ziyarci kasar Zimbabwe, da ganin yadda yaran kasar Zimbabwe suke yin rayuwa, suna bukatar gano ko akwai wata unguwa mai suna Mbare a duniya. Idan suka je wurin, bayan da suka dawo kasar Sin, za su kara samun karfin zuciya.”(Zainab)