logo

HAUSA

Sharhi:Wutar Olympics na haskaka duniya duk da duhun da ake ciki

2022-01-27 22:08:00 CRI

Sharhi:Wutar Olympics na haskaka duniya duk da duhun da ake ciki_fororder_QQ截图20220127220343

Samuel Ikpefan, shi ne dan wasan tseren yada kanin wani na dusar kankara na farko a Nijeriya, haka kuma dan wasan tseren dusar kankara na farko da ya shiga gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu a tarihin kasar. Yanzu haka, yana kokarin share fagen gasar Olympics na lokacin hunturu da nan ba da jimawa ba za a kaddamar a birnin Beijing. Idan ba a manta ba, yau shekaru hudu ke nan da suka wuce, tawagar Nijeriya da ke kunshe da ‘yan wasa mata uku ta halarci gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu na birnin Pyeongchang, karon farko da ‘yan wasan Nijeriya suka halarci gasar ta lokacin hunturu.

Sharhi:Wutar Olympics na haskaka duniya duk da duhun da ake ciki_fororder_073e2b3997ae49a69481f2079109eaef

Samuel ya ce, yadda ‘yan wasan Nijeriya suka halarci gasar a shekaru hudu da suka wuce a birnin Pyeongchang yana da muhimmiyar ma’ana, haka kuma ya karfafa masa gwiwa da ma sauran al’ummar Afirka.

Sakamakon yanayi mai dumi, akasarin kasashen Afirka ba su samu ci gaba sosai ba a wasannin kankara. Daga cikin kasashen Afirka 54, 15 ne kawai suka taba shiga gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu, sai dai hakan ba zai iya hana ‘yan wasa na kasashen Afirka ba, wadanda ba su son a bar su baya.

Ban da ‘yan wasa, kasashe daban daban na kara zura ido ga gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu na Beijing, wadanda suke fatan ganin gasar ta taimaka ga daidaita sabani da ma karfafa fahimtar juna da zumunci a tsakanin kasashe daban daban, musamman a lokacin da ake fuskantar koma bayan tattalin arziki a sakamakon annobar Covid-19 da ke addabar duniya da ma kalubale na nuna bangaranci da ma fin karfi.

Sharhi:Wutar Olympics na haskaka duniya duk da duhun da ake ciki_fororder_rBABC2HwsqKAEcwRAAAAAAAAAAA304.588x601

A ranar 25 ga wata, shugaban tarayyar Nijeriya, Muhammadu Buhari ya bayar da sanarwa, inda ya jaddada goyon bayansa ga gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu da za a gudanar a birnin Beijing. Ya ce, gasar wasannin Olympics dandali ne na karfafa zumunci da hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa, ya kuma yi fatan dukkan wasannin za su cimma burikan da ake fatan cimmawa na Olympics wajen daga matsayin ruhin wasanni, da karfafa zumunci, da kuma mutunta juna. Shi ma ministan harkokin wajen kasar Madagascar, Patrick Rajoelina, ya bayyana a kwanan baya cewa, wasannin Olympic tamkar wata muhimmiyar hanya ce ta daga matsayin hadin kan kasa da kasa. “Ta hanyar mutunta ruhin Olympic, za mu iya cimma nasarar hada mutane wuri guda ta hanyar kyakkyawar fahimtar juna da hadin kan kasa da kasa.”

Mutane da yawa daga kasashen Afirka sun bayyana adawarsu game da yadda wasu kasashe kalilan suke neman siyasantar da gasar don cimma burinsu na siyasa. Shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na kasar Zimbabwe Thabani Gonye, ya yi kakkausar suka kan yadda ake siyasantar da harkokin wasanni. Yana mai cewa, ba za a iya hada wasanni da siyasa ba. Ya kamata kasashen da abin ya shafa su mai da hankali a kan ‘yan wasansu, don taimaka musu cimma nasara a wajen gasar. Ya kara da cewa, ko da yake bai samu damar zuwa wajen gasar ba, amma shi da abokansa za su kasance a gaban talabijin, don karfafawa ‘yan wasan gwiwa.

Sharhi:Wutar Olympics na haskaka duniya duk da duhun da ake ciki_fororder_rBABCWHqD6iAJ3-8AAAAAAAAAAA30.640x360

Sanin kowa ne cewa, a cikin shekaru biyu da suka wuce, tattalin arzikin duniya ya dakushe a sakamakon annobar Covid-19, tare da haifar da rufe wa juna kofa da kawo baraka a tsakanin kasa da kasa. A sa’i daya, yadda wasu ‘yan siyasar kasashen yamma suka yi ta haifar da fito-na-fito a tsakanin kasa da kasa, ya kara tsananta halin da ake ciki. Wannan ya sa, a gasar wasannin Olympics na Tokyo da aka gudanar a bara, an kara saka kalmar “Together” cikin taken gasar Olympics, don ta zama “Faster Higher Stronger da ma Together”, wanda ya bayyana bukatun al’ummar duniya na karfafa hadin kansu don fuskantar kalubale.

Ruhin wasannin Olympics na bayyana cewa, duk irin kalubale da ake fuskanta, hadin kai shi ne babban makami ga dan Adam.

Sharhi:Wutar Olympics na haskaka duniya duk da duhun da ake ciki_fororder_641

A shekaru hudu da suka gabata, shugaban kwamitin wasannin Olympics na kasar Nijeriya, Habu Gumel ya bayyana cewa, wannan shi ne karo na farko da kasar Nijeriya ke halartar gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu, amma ba zai zama na karshe ba. Ya ce, “A gasar wasannin Olympics na Beijing, za mu ga sauye-sauye, ba kawai ta fannin wasannin da za mu halarta ba, har ma za mu samu karin ci gaba.” Yanzu haka, ‘yan wasa na kasashen Afirka suna kokarin share fagen gasar tare da takwarorinsu na sauran kasashen duniya, mu ma muna musu fatan cimma nasarori, muna kuma fatan su isar da sakon hadin kai ga al’ummun kasashen duniya.

Shugaban kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa, Thomas Bach ya ce, “Duk duhun da muka shiga, wutar wasannin Olympics za ta haskaka mana hanya don mu ga karshenta”. Nan da mako guda, za mu hadu a gasar wasannin Olympics, inda za mu rungumi makomarmu tare!