logo

HAUSA

Wasu ’Yan Siyasar Amurka Da Suka Bullo Da Wasu Dabaru Suna Kara Zama ‘Yan Bangar Siyasa

2022-01-26 20:27:00 cri

Wasu ’Yan Siyasar Amurka Da Suka Bullo Da Wasu Dabaru Suna Kara Zama ‘Yan Bangar Siyasa_fororder_微信图片_20220126202508

A cewar wasu majiyoyi, ma'aikatar harkokin wajen Amurka na duba yiwuwar ba da izinin janye jami'an diflomasiyyar ta da iyalansu daga kasar Sin, bisa la'akari da "tsauraran manufofi" na kasar Sin game da rigakafin cutar COVID-19. Yayin da kasa da kwanaki goma suka rage a bude gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi na birnin Beijing, wasu 'yan siyasa na Amurka na fakewa da irin wadannan dabaru, don neman bata manufofin rigakafin cutar ta kasar Sin, da kara haifar da sabani da rarrabuwar kawuna.

Da farko, sun sanar da cewa, ba za su tura jami'ansu zuwa gasar Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing ba, sannan sun soke zirga-zirgar jiragen sama da yawa daga Amurka zuwa kasar Sin da kamfanonin jiragen sama na kasar Sin suke yi, kuma a yanzu sun yada jita-jitar janye jami'an diflomasiyya da iyalansu daga kasar Sin. Duk wadannan matakan da suka dauka, sun sa duniya ta gano cewa, suna amfani da hanyoyi daban-daban wajen "kawo cikas" ga wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing, da yin Allah wadai da ruhin Olympics, da kuma gurgunta yanayin hadin kai a tsakanin kasashen duniya.

Yadda cutar COVID-19 ke yaduwa, ciki har da nau’in Omicron, ya sa kasar Sin ta gabatar da wasu tsauraran manufofi masu inganci na rigakafin kamuwa da cutar ta hanyar kimiyya, don kare dukkan 'yan wasa da ma'aikatan da ke da alaka, ya yadda za su iya halartar gasar, su kuma koma gida lafiya, wadanda ba shakka sun hada da ma'aikatan Amurka.

An lura cewa, a ranar 25 ga wata ne, aka rantsar da R.Nicholas Burns, sabon jakadan Amurka a kasar Sin. Don haka, ya kamata bangaren Amurka ya yi amfani da wannan dama, don kyautata dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, maimakon yin akasin haka. (Mai fassara: Bilkisu Xin)