logo

HAUSA

Hauhawar farashi a Amurka zai iya illata duk duniya

2022-01-26 17:16:16 CRI

Hauhawar farashi a Amurka zai iya illata duk duniya_fororder_src=http___res.cngoldres.com_upload_kuaixun_2021_0305_238cc3ee3fc80c16bcf416c7b60504e7.png&refer=http___res.cngoldres

Kafar yada labarai ta Fox News ta Amurka ta ba da rahoto a ranar 23 ga wata cewa, kaso 85 bisa 100 na Amurkawan da aka yi musu bincike sun bayyana damuwarsu game da hauhawar farashi a kasar. Rahoton da hukumar kwadago ta kasar ta fitar a ranar 12 ga wata, wanda ya nuna cewa 'ma'aunin farashin kayayyakin bukatun yau da kullum da mazauna birane ke saya wato CPI ya karu da kashi 7% a watan Disamba na shekarar bara, hakan ya sa yawan hauhawar farashi ya kai wani matsayi da ba a taba ganin irinsa ba tun daga shekarar 1982.

Shugaban kasar Amurka Joseph Biden ya taba cewa, babban bankin Amurka ya aiwatar da manufar kudi mafi sassauci a cikin shekara daya da rabi da suka gabata saboda matsin lambar da barkewar cutar COVID-19 ya haifar. Amma hakan ya haifar da buga takardun kudin Amurka mafi yawa, matakin da ya habaka gibin dake tsakanin masu wadata da matalauta. Ban da haka kuma, rashin daukar matakan da suka dace wajen dakile cutar ya sa tattalin arzikin Amurka yana fuskantar kalubalen koma baya da matsalar tsarin samar da kayayyaki, lamarin da ya sa al’ummar kasar ke matukar shan wahala. Saboda haka, masu goyon bayan Biden na kara raguwa, ‘yan siyasa na yin iyakacin kokarinsu don magance wannan matsalar. Shugaban babban bankin Amurka Jerome H. Powell ya taba bayyanawa a ranar 11 ga wata cewa, matsin lambar da hauhawar farashin ya haifar zai ci gaba da kasancewa har zuwa tsakiyar shekarar 2022. Hakan ya sa, bankin ya yanke shawarar kara kudin ruwa. Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya yi hasashe a ranar 20 ga wata cewa, babban bankin Amurka zai kara kudin ruwa sau 3 a wannan shekara.

Kara kudin ruwan wani mataki ne mai kyau wajen warware matsalar da Amurka ke fuskanta, amma zai illata sauran kasashe. An kira taron bidiyo na dandalin DAVOS a makon da ya gabata, inda babbar jami’ar IMF Kristalina Georgieva ta yi gargadi cewa, kasashe mafi karancin ci gaba na fuskantar matsalar basussuka saboda rashin hanzarin farfadowar tattalin arzikinsu. Idan babban bankin Amurka ya sanar da kara kudin ruwa, basukan da ake bin Amurka zai kara tsananta. Ta kara da cewa, yanzu yawan kasashen da suke fuskantar matsalar bashi ya ninka sau 2 bisa na shekarar 2015, matakin da ya haifar da mawuyancin hali ga tattalin arzikin duniya.

Abin da ya faru na bayyana cewa, matakan da gwamnatin Amurka ke dauka don farfado da tattalin arzikin cikin kasar na da burin fidda gwamnati daga mawuyancin hali na rashin daukar matakan da suka dace wajen dakile cutar COVID-19, amma buga takardun dala mafi yawa ya haifar da hauhawar farashi da tsananta rikici tsakanin masu wadata da matalauta. Hanya daya tilo da babban bankin Amurka zai dauka ita ce kara kudin ruwa, idan ba haka ba yawan al’ummar da ke goyon bayan gwamnati mai ci zai cigaba da raguwa matuka. Amma kara kudin ruwa zai illata tattalin arzikin sauran kasashe wadanda suke fuskantar mawuyancin hali a yanzu, matakin da Amurka ke dauka na dora matsalarta ga sauran kasashe.

Amma, da ganin irin wannan kalubale, matsayin da ‘yan siyasar Amurka ke dauka na da ban mamaki matuka. A ranar 24 ga wata, kafin wani taron minstocin kasar, dan jaridar Fox News, Peter Doocy, ya tambayi Biden cewa, ko hauhawar farashi zai zama wata matsalar siyasa kafin zabe? Biden ya ce: “What a great aset, more inflation…(Hauhawar farashi wata dukiya ce mai kyau ne)”, daga baya ya zargi wannan dan jarida da kalamai maras kyau. ‘Yan siyasa sun fahimci illar da matakin kara kudin ruwa zai haifar ga sauran kasashe, amma duk da haka suna ganin cewa, hauhawar farashi wata dukiya ne mai kyau, sabo da ba su damu da bukatun fararen hula da muradun sauran kasashe ba, duk da cewa hakan zai tilasta duk duniya biyan hasarar da gwamnatin ta haifar. (Amina Xu)