logo

HAUSA

Kasar Sin ta harba wani nau’in tauraron dan Adam

2022-01-26 14:13:10 CMG

Kasar Sin ta harba wani nau’in tauraron dan Adam_fororder_220126-B2-Tauraro

A yau Laraba, kasar Sin ta harba wani sabon tauraron dan Adam samfurin L-SAR-1-A zuwa sama. An yi amfani da rokar CZ-4C ta daukar kaya wajen harba wannan tauraron dan Adam mai kula da ayyukan binciken labarin kasa, da sa ido kan yanayin abkuwar wasu bala’u, irinsu zabtarewar kasa, da girgizar kasa, da dai sauransu.

Harbawar ita ce karo na 407 da aka yi amfani da rokar kwashe kaya  samfurin CZ-4C. (Bello Wang)

Bello